Zan yarda idan har na fadi zabe na gaskiya da amana – Atiku

Zan yarda idan har na fadi zabe na gaskiya da amana – Atiku

- Dan takarar shugaban kasa a jam’iyar PDP, Atiku Abubakar, yace zai yarda da kaye idan har ya fadi zaben 2019, wanda aka gudanar akan tafarkin gaskiya a amana

- Atiku ya ce a baya ma ya yarda da kaye balle a yanzu

- Ya bayyana hakan ne a wani shirin tattaunawa da wata yar jarida Kadaria Ahmed wanda aka haska a NTA

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar yace zai yarda da kaye idan har ya fadi zaben 2019, wanda aka gudanar akan tafarkin gaskiya a amana.

Mista Abubakar yace ya amince da kaye a lokacin da ya fadi a baya sannan bai ga dalilin da zai sa wannan zai zamo mai wahala ba.

Mista Abubakar ya fito ne a wani shirin gidan talbijin na yan takara da yar jarida Kadaria Ahmed ta gudanar a NTA a daren ranar Laraba, 30 ga watan Janairu. Mataimakin Atiku, Peter Obi ma ya halarci taron.

Zan yarda idan har na fadi zabe na gaskiya da amana – Atiku

Zan yarda idan har na fadi zabe na gaskiya da amana – Atiku
Source: UGC

Abubakar shine babban dan adawar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben Shugaban kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Amsar da Atiku ya bayar ya sha bambam da wanda shugaba Buhari ya bayar a baya lokacin da aka yi masa makamanciyar wannan tambayan a farkon watan nan.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Arewa ta marawa Buhari baya akan dakatar da Shugaban alkalan Najeriya

Miss Ahmed ta tambayi Buhari ko zai amshi kaye, amma maimakonyace eh ko a’a, Shugaban kasar ya bayar da amsa a baude.

Ko da dai yayi tuni ga zabensa na ya fadi a baya, inda yace hakan ya faru ne saboda an cuce shi, amma ba wai don jama’a ba su zabe shi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel