Tsohon babban Sakataren kudin PDP na Najeriya ya koma Jam’iyyar APC

Tsohon babban Sakataren kudin PDP na Najeriya ya koma Jam’iyyar APC

- Shugaban kasa Buhari ya karbi wasu tsofaffin ‘Yan PDP da su ka dawo APC

- Wani Jigo na Jam’iyyar PDP da Magoya bayan sa sun tattara sun dawo APC

- A jiye ne Shugaban kasar ya karbi Bolaji Anani da mutanen sa a Garin Kalaba

Tsohon babban Sakataren kudin PDP na Najeriya ya koma Jam’iyyar APC

Wani Jigon PDP ya sauya-sheka zuwa APC a Kuros Riba
Source: Facebook

Mun ji cewa a jiya Laraba 30 ga Watan nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci Garin Kalaba a cikin jihar Kuros-Riba inda ya karbi wadanda su ka sauya-sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulkin kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da sauyin-shekar Bolaji Anani da dinbin magoya bayan sa da su ka dawo cikin tafiyar jam’iyyar APC. Buhari ya karbi sababbin ‘yan APC din ne a filin wasa na U.J Esuene da ke garin Kalaba.

KU KARANTA: 2019: Sarkin Aba yayi watsi da Atiku ya kama jirgin Buhari

Bayan karbar ‘yan siyasan da su ka sauya-sheka daga jam’iyyar hamayya, shugaban kasar yayi wa mutanen Kuros-Riba alkawari cewa zai dawo jihar su da zarar ya lashe zabe. Jama’a da-dama na Jihar dai sun yi watsi da PDP zuwa APC.

Da alamu dai shugaban kasar yana da tabbacin samun nasara a zaben da za ayi kwanan nan inda yake bayyana cewa zai sake lekowa jihar bayan ya lashe zabe. Buhari yana sa ran doke sauran abokan gabar sa a zaben na 16 ga watan gobe.

Kafin nan dai an ji cewa wasu ‘ya ‘yan Jam’iyyar PDP fiye da 2500 su ka tsere daga jam’iyyar hamayyara su ka dawo APC domin taya shugaban kasa Muhammadu Buhari yakin tazarce a babban zaben bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel