2019: Jam’iyyar APC ta shirya tafka magudi a Ogun inji Gwamna Amosun

2019: Jam’iyyar APC ta shirya tafka magudi a Ogun inji Gwamna Amosun

- Rikicin Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Ogun yana kara fitowa fili

- Gwamna Ibikunle Amosun ya zargi APC da shirin murde zaben Ogun

- Mai girma Gwamnan Jihar yace wannan shiri sam ba zai kai labari ba

2019: Jam’iyyar APC ta shirya tafka magudi a Ogun inji Gwamna Amosun

Gwamnan Ogun ya ja kunnen APC a game da shirin murde zabe
Source: Depositphotos

Mun samu labari cewa rikicin cikin gidan da ake yi a jam’iyyar APC yana cigaba da kara kamari inda har ta kai gwamna Ibekunle Amosun ya fito fili yana cewa jam’iyyar APC mai mulki ta na da shirin murde zaben da za ayi bana.

Gwamna Ibikunle Amosun wanda yanzu yake neman komawa majalisar dattawa, ya bayyana cewa ana yunkurin murde zaben gwamna a jihar ta Ogun. Amosun yake cewa wannan mugun nufi da ake shiryawa ba zai ko ina ba.

Sanata Ibikunle Amosun yayi wannan bayani ne a farkon makon nan a lokacin da ya halarci wani zaman coci domin taya babban Limamin Kiristoci na Legas, Rabaren Dr. Michael Olusina Fape murnar cika shekaru 60 a Duniya.

KU KARANTA: Matasan Kano sun ja kunnen Buhari a kan taba babban Alkalin kasa

Yanzu dai gwamnan mai shirin barin gado yana rikici da jam’iyyar sa ta APC mai mulki inda ya tsaida ‘dan takarar sa watau Adekunle Akinlade a karkashin jam’iyyar APM bayan ya rasa tikitin jam’iyyar APC a kwanakin baya.

Yanzu ‘dan takarar gwamnan zai yi wa APC adawa a zaben jihar Ogun da za ayi domin ganin Honarabul Adekunle Akinlade ya gaje sa. Gwamnan duk da yana neman Sanata a APC, yana kokarin ganin APC ta fadi zabe a Jihar Ogun.

Gwamnan dai ya ja kunnen APC da cewa su daina tunanin cewa za su iya murde zabe a jihar Ogun inda yace babu wanda ya isa ya hana mutanen yankin yammacin jihar Ogun fitar da gwamna wannan karo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel