Ba zan damu ba idan aka kayar da ni a zaben gaskiya da gaskiya – El-Rufai

Ba zan damu ba idan aka kayar da ni a zaben gaskiya da gaskiya – El-Rufai

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa ba zai damu ba idan har ya fadi zaben shekarar 2019 matukar an gudanar da zaben cikin gaskiya da gaskiya, ba tare da kaci baka ci ba, baka ci ba, ka ci.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wani taro da hukumar zaman lafiya ta jahar Kaduna ta shirya da hadin gwiwar kungiyar zaman lafiya ta kasa da kuma majalisar dinkin duniya.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe yan ta’adda 4 a wata karanbatta a Borno

A jawabinnasa, El-Rufai yace babban abin dake da muhimmanci ga gwamnatin jahar Kaduna shine gudanar da mulkin adalci tare da tabbatar da an gudanar da zaben 2019 cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

“Bari na fada muku, a madadina da gwamnatin jahar Kaduna, babban abinda muka sanya a gaba shine gudanar da mulki a jahar, abinda nake nufi da mulki shine tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yayin zabe da bayan zabe.

“Mun yi rantsuwar gudanar da mulkin jahar da gaskiya da adalci, kuma zamu cigaba da yin haka har zuwa ranar 29 ga watan Mayu 2019, koda kuwa mun ci zabe ko bamu ci ba, idan kuma an sake zabenmu, zamu cigaba da yin iyaka kokarinmu.

“Idan kuma ba’a zabemu ba zamu cigaba da tafiyar da rayuwarmu, ba siyasa bace aikin da muka yi kadai ba, wannan shine dalilin da yasa muke son rattafa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, babu maganan a mutu ko ayi rai a siyasa, muna kamfe da ayyukan da muka yi ma jama’a ne, don haka babu damuwa idan muka fadi zabe matukar ba kwace zaben aka yi ba.” Inji shi.

Da yake nasa jawabin, wakilin majalisar dinkin duniya, Mohamed Ibn Chambas ya bayyana muhimmancin ganin Najeriya ta tsallake zaben 2019 cikin kwanciyar hankali, fiye da wanda aka samu a 2015.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel