Zan dauki tsatstsauran matakai akan kwamandojin rundunar Sojin Najeriya –Atiku

Zan dauki tsatstsauran matakai akan kwamandojin rundunar Sojin Najeriya –Atiku

Dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai dauki tsatstsauran mataki akan duk wani kwamandan rundunar Sojin Najeriya da yayi sake har yan Boko Haram suka samu galaba akan Sojojinsa, ko kwace makamansu.

Atiku ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da wata yar jarida, Kadari Ahmed a daren Laraba, 20 ga watan Janairu, inda yace kafin ya dauki wannan mataki, sai ya fara inganta walwalar Sojojin Najeriya, tare da basu horon daya dace.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun kashe yan ta’adda 4 a wata karanbatta a Borno

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi yana cewa ba zai lamunci yadda manyan kwamandojin Soji ke nuna gazawa ba, duk da cewa sun samu dukkanin aikin da suke bukata a yakin da Najeriya ke yi da yan ta’adda.

“Idan har na baku makaman da suka kamata, amma kuka bari yan ta’adda suka samu galaba akanku, toh tabbas zan dauki tsatstsauran mataki akanku, abinda yasa muke samun koma baya a yakin shine saboda ba’a hukunta duk wanda aka kama da laifin rashawa.

“Haka zalika ina ganin rashin kayan aiki ma na daga cikin manyan matsalolin da Sojoji suke fuskanta, don haka zamu tabbatar da mun samar da isassun kayan aiki, amma fa ba zamu ga karshen yakinnan ba idan Sojoji suka cigaba da tafka asaran makamansu a hannun Boko Haram” Inji shi.

An samu karuwar ayyukan kungiyar Boko Haram a yan kwanakin nan, wanda ya sabbaba mutuwar daruruwan Sojoji, sai dai yan Najeriya da dama sun zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashin ladabtar da shuwagabannin Sojoji, musamman wadanda ake ganin da hannunsu a cikin badakalar.

Sai dai shugaba Buhari yace bai ga dalilin tsige shuwagabannin Sojin ba, inda yace koda aikin da suke yi bai kai ga abinda yake tsammani ba, amma bai dace a cire shuwagabannin Soji a lokacin da ake tsaka da yaki ba.

Tun a shekarar 2017 wa’adin mulkin shugaban hafsoshin sojan Najeriya, Janar Abayomi Olanisakin da na babban hafsan sojan kasa, laftanar janar Tukur Buratai ya kare, amma Buhari ya kara musu wa’adi.

Bugu da kari Atiku ya zargi Sojoji da shiga sharo ba shanu a rikicinsu da yan shia daya gudana a watan Disambar shekarar 2015, inda yace ba aikin Soja bane rikici da yan shia, aikin Dansanda ne, a cewarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel