2019: Manyan abubuwan da Atiku ya fada wajen hirar da aka yi da shi

2019: Manyan abubuwan da Atiku ya fada wajen hirar da aka yi da shi

Jiya ne aka yi hira da ‘dan takarar jam’iyyar PDP na shugaban kasa, Atiku Abubakar da kuma mataimakin sa watau Peter Obi. ‘Yan takarar sun bayyana abubuwa da-dama a shirin na #TheNGCandidates da Kadaria Ahmed ta shirya.

Hukumar gidan talabijin na Nigerian Television Authority (NTA) da kuma hadin-gwiwar Daria Media da gidauniyar MacArthur Foundation su ka shirya wannan tattaunawa inda ‘yan takarar su ka gana da jama’a a wani dakin taro a Garin Abuja.

Mun kawo abubuwan da ‘dan takaran ya tattauna a kai.

2019: Manyan abubuwan da Atiku ya fada wajen hirar da aka yi da shi

Atiku yace zai cigaba da yaki da barayi idan ya samu mulki
Source: Twitter

1. Zargin satar makudan kudi

Atiku Abubakar ya musanya cewa an taba kama sa da laifin wawurar kudi a lokacin yana aiki a hukumar kwastam da kuma gwamnati. Atiku ya kuma karyata cewa ana neman Mai dakin sa a Amurka saboda zargin satar kudi.

2. PDP ta sha kasa a zaben 2019

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai yi na’am da sakamakon zaben 2019, muddin idan ba a tafka magudi da murdiya a zaben ba. Atiku ya bayyana cewa ba yau ya fara yin takara ya kuma sha kasa ba don haka zai rungumi kaddara.

3. Saida kadarorin Gwamnati

An zargi PDP da jawowa Najeriya asara wajen saida kadarorin kasar. Sai dai Atiku ya bayyana cewa ba za ace ba ayi nasara ba, sai dai a iya cewa an samu matsalolin da ba za a rasa ba, amma yana mai yakinin cewa an ci riba.

KU KARANTA: Zan duba yiwuwar yafewa barayin Najeriya idan na ci zabe - Atiku

4. Yaki da cin hanci da rashawa

Atiku ya nuna cewa idan ya zama shugaban kasa za a cigaba da yakar barayi. Atiku ya kuma bayyana cewa zai iya bada lamuni ga barayin kasar su maido dukiyar da su ka sace sannan kuma ya kawo gyara a bangaren shari’ar.

5. Rikicin Shi’a da Jami’an tsaro

‘Dan takarar na PDP yayi tir da irin takaddamar da aka rika samu tsakanin Mabiya Shi’a da Sojojin Najeriya wanda ya jawo rasuwar rayuka. Atiku yace bai kamata a aikawa ‘Yan shi’a Sojoji a lamarin da bai wuce na ‘Yan sanda ba.

6. Yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram

Atiku Abubakar yayi magana game da rikicin Boko Haram inda yace ana samun cikas ne saboda rashin makamai, yana mai alwashin cewa zai gyara wannan matsala. Sannan Atiku yace zai hukunta duk Sojan da ya samu da laifi.

7. Rikicin Manoma da Makiyaya

Atiku a matsayin sa na Fulani, ya bayyaba cewa yadda za a kawo karshen rigimar da ake fama da ita tsakanin Makiyaya da Manoma shi ne Makiyayan su zauna wuri guda su rika kiwo. Atiku yace an taba samun irin wannan rikici har a Amurka.

KU KARANTA: Atiku zai kashe makudan kudi wajen yin hanyoyi idan PDP ta ci zabe

8. Magudin zabe a Najeriya

Alhaji Atiku Abubakar ya kuma bayyana cewa magudi da murdiya da ake yi na zabe duk yana cikin rashin gaskiyar da ake fama da ita a kasar. Atiku yace zai kafa hukuma domin magance wannan da kuma rage satar kudin gwamnati.

9. Gwamnatin Buhari

A cewar babban ‘dan hamayyar, gwamantin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza cika alkawuran da ta dauka a baya na yaki da cin hanci da rashawa da kuma kawo karshen matsalar taro da bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

10. Maganin talauci da bara

An tambayi Atiku irin kokarin da yake yi na kawo karshen barace-barace da almajiranci a yankin sa inda yace ya tabuka wani abu. Atiku ya kara bada tabbacin cewa babban burin sa shi ne samawa jama’an Najeriya aikin yi idan ya samu mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel