Zaben 2019: Atiku Abubakar ya kaso jirgin karyar jam'iyyar APC

Zaben 2019: Atiku Abubakar ya kaso jirgin karyar jam'iyyar APC

Dan takarar kujerar shugaban kasar Najeriya a karkashin tutar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya ce karyace tsagwaron gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke shirgawa na cewa kasar na ta saida gangar danyen mai $100 a shekara 16 da suka yi suna mulki.

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa maganar gaskiya Shugaba Goodluck Jonathan ce kadai ta saida danyen man a wannan farashin a kuma dan wani lokacin da yayi yana mulki na shekaru biyu kacal.

Zaben 2019: Atiku Abubakar ya kaso jirgin karyar jam'iyyar APC

Zaben 2019: Atiku Abubakar ya kaso jirgin karyar jam'iyyar APC
Source: Twitter

KU KARANTA: Zan duba yiyuwar yafewa barayin Najeriya - Atiku

Legit.ng Hausa ta samu cewa Atiku ya bayyana hakan ne a yayin da yake ansa tambayoyi a wata fira na musamman da 'yar jarida Kadaria Ahmad tayi da shi kai tsaye aka kuma watsa a tashohi da dama a ranar Laraba.

Atiku Abubakar kamar yadda muka samu ya kara da cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya hau mulki ne a lokacin da gangar danyen man take $11 kuma ya fidda kasar daga matsin tattalin arzikin kasa sannan ya biyawa kasar bashin da ake bin ta.

Haka zalika Alhaji Atiku ya bayyana salon mulkin APC da shugaba Buhari a matsayin wanda ba sanin makama wanda hakan ne ma ya jefa kasar cikin halin da take ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel