Rana-bata-karya: Shugaba Buhari zai yi ido hudu da Gwamna Ganduje a Kano

Rana-bata-karya: Shugaba Buhari zai yi ido hudu da Gwamna Ganduje a Kano

A cigaba da yawon gangamin yakin neman zaben sa, a ranar Alhamis ne dai ake sa ran shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, zai je jihar Kano dake a yankin Arewa maso yammacin Najeriya mai tarin jama'a.

Sai dai zuwan na Shugaba a jihar yana zuwa ne a daidai lokacin da takaddama a tsakanin 'yan siyasa, kungiyoyin sa kai da sauran al'umma a ciki da wajen jihar, a kan hotunan bidiyon, da ake zargin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da karbar rashawa.

Rana-bata-karya: Shugaba Buhari zai yi ido hudu da Gwamna Ganduje a Kano

Rana-bata-karya: Shugaba Buhari zai yi ido hudu da Gwamna Ganduje a Kano
Source: Twitter

KU KARANTA: Idan na mutu Buhari ne sila - Gwamna Ortom

Legit.ng Hausa haka zalika ta samu cewa duba da muhimmancin wannan ziyara ga shugaban kasar da gwamnan jihar, al'umma ya zuwa yanzu sun zura ido ne don ganin yadda taron zai kasance.

Magoya bayan gwamnan jihar, na fatan cewa wannan ziyara ta shugaba Buhari, za ta kawo karshen rade-radin tsamin dangantakar da ake zargi ta shiga tsakanin Ganduje da Buhari.

Wasu dai na cewa wai shugaban kasar a yanzu, baya ma son hada hanya da gwamnan na Kano, ballantanama har ya sake daga hannunsa ya ci zabe.

Yanzu dai an zura ido ne a gani shin shugaban kasar zai daga hannun gwamnan a matsayin sa na dan takarar jam'iyyar APC a jihar kamar yadda al'adar gangamin yakin neman zaben take ko kuma ya kyale shi duba da zarge-zargen dake a wuyan sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel