Onnoghen: Ana ta zanga-zanga a Landan domin nuna goyon baya ga Shugaba Buhari

Onnoghen: Ana ta zanga-zanga a Landan domin nuna goyon baya ga Shugaba Buhari

- Ana ta faman zanga-zanga a cikin Landan saboda dakatar da CJN Walter Onnoghen

- Masu zanga-zangar sun yi tir da masu neman a maida Onnoghen kan mukamin sa

- Kwanaki ne Shugaba Buhari ya dakatar da babban Alkalin Akalan Najeriya daga ofis

Onnoghen: Ana ta faman zanga-zanga a Landan domin nuna goyon baya ga Shugaba Buhari

Zanga-zanga ya barke a cikin kasar Ingila a dalilin cire Onnoghen
Source: UGC

Mun ji cewa ana ta zanga-zanga a birnin Landan a dalilin babban Alkalin Najeriya Mai shari’a Walter Onnoghen da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a dalilin zargin da ke wuyan sa na tara wasu makudan kudi a asusun sa.

Wasu sun nuna cewa wannan abu da shugaban kasa Buhari yayi, yayi daidai domin kuwa an kama hanyar gyara kasar. Masu zangar-zangar sun yi Allah-wadai da kiran da wasu su ke yi na cewa a maida Walter Onnoghen kan kujerar sa.

KU KARANTA: Wasu 'Yan Arewa sun goyi bayan dakatar da Shugaban alkalan Najeriya

Wadannan Bayin Allah da su ka fito su na zanga-zanga a kan titunan Ladan sun tafi har kusan gidan Firayim Ministar Birtaniya da ke kan layin Downing Street a Landan su na masu neman kasar ta Ingila ta dafawa gwamnatin Buhari.

Wani mutumin Najeriya mai suna Andrew Kobani, ya nemi a taimakawa shugaban kasa Buhari wajen ganin ya gyara kasar nan. Kobani yace tububuke babban Alkalin kasar da aka yi, ya nuna kokarin gwamnatin Buhari na kawo gyara.

Andrew Kobani yayi kira ga Theresa May ta agazawa gwamnatin Najeriya wajen yaki da rashin gaskiya. Kobani ya babban Alkalin kasar rashin gaskiya a shari’ar sa da ake yi a kotu wanda yace ana neman a jefawa rigar addini da kabilanci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel