Zan kashe kusan Tiriliyan 10 wajen gina abubuwan more rayuwa – Atiku

Zan kashe kusan Tiriliyan 10 wajen gina abubuwan more rayuwa – Atiku

- Atiku zai yi kokarin tada hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa a Najeriya

- ‘Dan takarar yace zai kashe biliyan $25 wajen gina tituna idan har ya samu mulki

- Atiku na PDP ne dai babban kalubalen da tazarcen Buhari zai samu a zaben bana

Zan kashe kusan Tiriliyan 10 wajen gina abubuwan more rayuwa – Atiku

Atiku yace Gwamnatin sa za ta batar da domin ayi tituna a Najeriya
Source: Facebook

Mun samu labari daga jaridun kasar Turai cewa ‘dan takarar jam’iyyar PDP na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya sha alwashin gina hanyoyi da inganta tituna muddin ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa.

‘Dan takarar babbar jam’iyyar hamayyar kasar ya bayyana cewa zai kafa wata gidauniya ta musamman da za ta ji da batun gina hanyoyi a fadin Najeriya. Atiku ya bayyana wannan ne ta wani sako da ya aikawa wani gidan jarida.

KU KARANTA: 2019: Sarkin Aba yayi watsi da Atiku ya kama jirgin Buhari

Atiku Abubakar yana mai alkawarin cewa idan jam’iyyar sa ta PDP ta samu mulki, zai hada kai da ‘yan kasuwa wajen ganin an kafa wani asusu da zai ci Dala biliyan 25 domin gina hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa.

Babban Abokin hamayyar na shugaban kasa Buhari a zaben 2019, yace gwamnatin sa za ta nunka yawan kudin da Najeriya ta ke kashewa wajen gina hanyoyi. Atiku yace za a cin ma wannan buri ne daga yanzu zuwa shekarar 2025.

Atiku Abubakar mai shekaru 72 a Duniya zai kara ne da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yake neman tazarce a kan mulki. Atiku yana ganin cewa dole gwamnati ta hada kai da ‘yan kasuwa domin a kai ga ci a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel