Mutanen Ibo sun karbi Buhari da hannu biyu – Fadar Shugaban kasa

Mutanen Ibo sun karbi Buhari da hannu biyu – Fadar Shugaban kasa

A makon nan ne jirgin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga kasar Ibo inda ya zagaya zuwa jihar Abia da kuma Imo domin ganin ya samu goyon bayan jama’a a zaben bana.

Mutanen Ibo sun karbi Buhari da hannu biyu – Fadar Shugaban kasa

Sarakin Aba ya nemi jama’a su zabi Shugaban kasa Buhari
Source: Facebook

A wajen yawon yakin neman zaben, shugaban kasa Buhari ya samu gagarumar goyon baya daga mutanen yankin na Kudu maso gabas. Fadar shugaban kasar ta bayyana wannan ta bakin babban hadimin shugaba Buhari watau Garba Shehu.

Malam Garba Shehu ya bayyana cewa shugaba Buhari ya samu goyon baya ne daga shugaban Sarakunan kasar Aba watau Mai martaba Isaac Ikonne mai kasar Aba na I. babban Sarkin ya nemi mutanen sa su marawa APC baya a zaben bana.

KU KARANTA: Na san siyasa da kasuwanci shiyasa na ke takara - Atiku

Babban Sarkin ya bayyana cewa mutanen sa za su zabi shugaba Buhari ne saboda irin abin da gwamnatin nan tayi masu. Daga cikin kokarin shugaba Buhari akwai biyan tsofaffin Sojojin Biyafara kudin su da kuma gyara harkar kasuwanci.

Bayan nan kuma Sakataren kungiyar nan ta Inyamuran Najeriya ta Ohanaeze Ndigbo, watau Uche Okwukwu, yayi kira ga jama’a su marawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar APC mai mulki baya a zaben da za ayi kwanan nan.

KU KARANTA: Za a ji El-Rufai yana sukar Buhari nan gaba kadan inji Sanatan Arewa

Uche Okwukwu wanda yana cikin manyan kasar Inyamurai ya tabbatar da cewa ba su tare da jam’iyyar PDP mai adawa. A baya dai shugaban kungiyar ya nuna cewa kungiyar Ohanaeze Ndigbo za ta zabi Atiku Abubakar ne kafin Sakataren yayi masa raddi.

Okwukwu ya bayyana cewa kungiyar za ta zo har fadar shugaban kasa domin fadawa Duniya cewa mabiyan ta za su zabe sa. Haka kuma gwamnan jihar Abia ya nuna jituwar da ke tsakanin sa da shugaba Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel