Martanin gwamnati kan labaran dake zuwa daga Katsina kan kafa tutar 'yan ta'adda

Martanin gwamnati kan labaran dake zuwa daga Katsina kan kafa tutar 'yan ta'adda

- Rahotanni ke ta yawo wai masu ta'adda sun kafa tuta a karamar hukumar Kankiya

- Hukumomi sun karyata hakan

- Matsalar tsaro tayi wa Katsina katutu a watannin nan

Martanin gwamnati kan labaran dake zuwa daga Katsina kan kafa tutar 'yan ta'adda

Martanin gwamnati kan labaran dake zuwa daga Katsina kan kafa tutar 'yan ta'adda
Source: Depositphotos

Ofishin kwamishinan 'yansanda na jihar Katsina, ya karyata jita-jita dake yawo cewa wai an sami wasu gungun mutane dake garkuwa da mutane da wai suka kafa tuta a jihar Katsinar a kauyuka dake karamar hukumar Faskari.

SP Gambo Isah, kakakin hukumar ne ya bayyana matsayin ofishinsu kan batun, inda yace babu gaskiya a labarin domin kuwa hukuma na ko'ina ya yankin na Katsina.

Wata jarida ce ta Intanet mai sunan Jaridar Taskar labarai ta yayata labarin, inda tace 'yan ta'adda sun kame kauyukan karamar hukumar Faskari, sun saci mutane sun kuma kafa tutarsu a jiya laraba, wai a kauyuka biyar a Faskari LGA.

GA WANNAN: Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ya harbo sabbin masu linzami daga Legas

Jaridar, ta lissafta kauyukan a haka: Unguwar Tsamiya, Birnin Kogo, Raba, Zuru da Unguwar Doka, ta kuma ce masu dauke da makaman, sun yiwa mutane kashedi, kan kada su sake su bari bakin fuskoki su shigo musu daga hukuma.

A cewar 'yansanda, kowa ya ci gaba da harkokinsa, babu gaskiya a lamarin, kuma babu wasu 'yan ta'adda a jihar ta Katsina.

An dai sami irin wannan a baya a jihohi masu alaka da Nijar, inda aka jiyo wasu 'yan ta'adda na karbar haraji kuma suna kafa tutocin jihadi a yankin, kain hukuma ta kore su.

Gwamna Masari ma dai, ya koka kan yadda masu kisan gilla a Zamfara ke yi wa jiharsa kawanya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel