Chabb! Shekararta 14 kacal amma ta iya satar N3.5m, an sanya ta kurkuku

Chabb! Shekararta 14 kacal amma ta iya satar N3.5m, an sanya ta kurkuku

- An yankewa yarinya yar shekaru 14 hukuncin zaman gidan yari na shekara 1

- An kamata dumu dumu da laifin satar kudi har Naira miliyan 3.5

- Shugabar makarantar ta ce ta sanyata tare da mata alkawarin cewa zata kaita kasar waje don cigaba da karatu

An yankewa wata yarinya yar shekaru 14 hukuncin shekara daya a gidan horon yara sakamakon satar Naira miliyan 3.5 da tayi daga uwargidanta.

An yankewa yarinyar hukunci ne tare da shugaba kuma mai makarantarsu. Makarantar ta kudi ce dake Kano mai suna Shola Ogedegbe.

Mai shari'a Mukhtar Dandago, yace kodai tayi zaman gidan horon ko kuma ta biya tarar dubu hamsin.

An gurfanar da yarinyar mai shekaru 14 ne da zargin aikata laifuka hudu da suka hada da balle gida da sata, Inda aka zargi shugabar makarantar da karbar kayan satar.

Kotun taji cewa anja hankalin yarinyar ne tayo satar da alkawurran karya na cewa za a kaita kasar waje ta cigaba da karatunta wanda shugabar makarantar tayi mata.

Shugabar makarantar har yanzu dai tana gaban kotu akan laifin ta na karbar kayan satar.

Chabb! Shekararta 14 kacal amma ta iya satar N3.5m, an sanya ta kurkuku

Chabb! Shekararta 14 kacal amma ta iya satar N3.5m, an sanya ta kurkuku
Source: Getty Images

Kamar yanda FIRST ya kaiwa kotun, Mr Olayinka Dagunduro ta titin Zungeru , Sabon garin Kano ta kai kara ga ofishin yan sanda dake Kwakwachi a Kano, cewa wani lokaci a tsakanin watan Octoba da November 2018 cewa yarinya ta shiga gidanshi ba izini, ta balle dakinshi tare da sace Naira miliyan 3.5.

GA WANNAN: Majalisin Alkalan kasar nan (NJC) kawai ya sallami Onnoghen - Falana

Yace da ya bincika ya gano cewa har da hadin bakin mamallakiyar makarantar Shola Ogedegbe.

Yarinyar da ake zargin ta sanar da kotun cewa shugabar makarantar ta ce tasa ta sato kudin daga ubangidanta don kafa kamfanin siminti kuma da tabbatar mata cewa bayan ta gama sakandire za ta kaita jami'a kasar waje don cigaba da karatunta da ribar.

Mai shari'a Mukhtar Dandago ya daga sauraron karar shugaban makarantar zuwa 5 ga watan Fabrairu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel