Bayan mun ci zabe: Zamu hukunta masu magudi daga kowacce jam'iyya - Atiku/Obi

Bayan mun ci zabe: Zamu hukunta masu magudi daga kowacce jam'iyya - Atiku/Obi

- Atiku yayi alkawarin samar da ofishin hukunta masu almundahanar zabe

- Yace rashin kayan aiki da walwala ke kawo cibaya a harkar sojin kasar nan

- Matuakar aka zabe ni zan farfado da harkar ilimin fulanin tashi, inji Atiku

Limamin Coci zai dauki Almajirai ya k3oya musu sana'a, Limaman Musulmi sunce anqi wayon

Limamin Coci zai dauki Almajirai ya k3oya musu sana'a, Limaman Musulmi sunce anqi wayon
Source: Facebook

Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar a ranar laraba yayi alkawarin samar da ofishin almundahanar zabe don gurfanar da duk wanda ya karya dokar zabe.

Atiku yace gwamnatin yanzu bata da dokokin hukunta masu laifin.

Yace shi da mataimakin shi Peter Obi suna da duk abinda yakamata mutum ya mallaka don yaki da talauci a kasar nan.

Yace yayi kokarin fitar da mutane 45,000 daga jihar Adamawa daga talauci.

"Shekaru kadan da suka wuce, na kirkiro bankin bada bashi sannan na samu wani daga Bangladesh, kun san sun kware a harkar. Na sanar dashi ina son fitar da mutane daga talauci kuma kashi 80 na bashin da za a bada ya zamana mata ake bawa. Kunsan mutane nawa na fitar daga talauci? 45,000," inji shi.

GA WANNAN: Dakatar da Alkalin Alkalai: Buhari yayi wa tayar wasu tsiraru faci ne suna tsaka da kissa

Tsohon mataimakin shugaban kasar yace Najeriya na bukatar kasuwanci da bangarori masu zaman kansu don samar da aiyuka miliyan 21 ga matasa marasa aikin yi.

Kamar yanda yace, daya daga cikin shirye shiryen shi na samar da aiki shine infanta bangaren noma da kiwo wanda ke da kaso mafi yawa na samar da aiki a kasar nan.

Fin rabin biliyan PenCom ta kwato wa masu Fansho daga guminsu na karshen 2018

Akan zargin rashawa yace shine ma'aikacin da aka fi bincike akan kowa a kasar nan amma har yanzu ba a kama shi da laifi ba.

Yayi jajen durkushewar yan Najeriya masu rufin asiri kuma ya dora laifin ga gwamnatin shugaban kasa Buhari akan rushewa da durkushewar masu masakaicin karfi.

Akan Boko Haram, yace abin da ya kawo ci baya ga sojin Najeriya shine kayan aiki da walwala.

Idan aka zabe shi, yayi alkawarin bincikar abinda ke kawo ci baya ga sojin kasar nan.

Akan fadan yan shi'a da sojoji, yace soja basu da hadin komai dasu. Da anbar yan sanda sun yi abinda ya dace.

Akan fadan manoma da makiyaya kuwa, yace akwai bukatar dukkanin su a wayar musu da kai akan dokokin kasa.

Yayi jajen rushewar ilimin fulanin tashi inda yayi alkawarin farfado dashi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel