Ba ni da ikon yaye talauci a jihar Adamawa - Atiku

Ba ni da ikon yaye talauci a jihar Adamawa - Atiku

A jiya Laraba 30 ga watan Janairu, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya yi karin haske dangane da kangi da kuma katutu na fatara da talauci da al'ummar jihar Adamawa ke fuskanta duk da kasancewar ta Mahaifar sa.

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubalar, ya ce ba ya da laifi kuma ba za a zarge shi ba a sakamakon katutu na talauci da al'ummar jihar Adamawa ke fuskanta duk da ta kasance Mahaifar sa.

Ba ni da ikon yaye talauci a jihar Adamawa - Atiku

Ba ni da ikon yaye talauci a jihar Adamawa - Atiku
Source: Twitter

Atiku ya hau kujerar naki ta daukar nauyi da kuma rashin karbar laifi na gazawa ta fuskar yaye talaucin da al'ummar jihar Adamawa ke fuskanta duk da ya kasance daya daga cikin manyan ababe biyu masu samar da aikin yi a jihar.

Atiku ya ce kasancewar sa na biyun gwamnatin jihar Adamawa ta fuskar samar da aikin yi ga al'umma, ba ya nufin hakan zai yaye ma su talauci domin kuwa mutum guda ba ya da ikon yaye wa kowace al'umma talauci.

KARANTA KUMA: Kwarewa ta akan siyasa da kasuwanci ya sanya na ke takarar kujerar shugaban kasa - Atiku

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Atiku ya yi wannan karin haske yayin zaman sauraron ra'ayin al'umma da ya gudana a babban birnin kasar nan na tarayya wanda gidan Talabijin na kasa wato NTA ya dauki nauyin shiryawa.

Wazirin Adamawa, ya kuma kausasa harshe kan gazawar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar samar da ingataccen tsaro musamman a yankunan Arewacin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel