Da baka zama Shugaban kasa ba idan ba don US, da UK ba – Tsohon jigon APC ga Buhari

Da baka zama Shugaban kasa ba idan ba don US, da UK ba – Tsohon jigon APC ga Buhari

- Tsohon mataimakin sakataren labarai na jam’iyyar APC, Comrade Timi Frank, yace da Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai zamo Shugaban kasar Najeriya ba a 2015 idan ba don kasashe kamar su Amuka da Ingila sun sanya baki ba

- Frank ya yi kira ga kasashen duniya da su yi watsi da shugabancin Najeriya da shugabannin jam’iyyar APC mai mulki

- Ya yi kira ga kasashen da su taimaka wajen wanzar da damokradiya a Najeriya

Tsohon mataimakin sakataren labarai na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Comrade Timi Frank, yace da Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai zamo Shugaban kasar Najeriya ba a 2015 idan ba don kasashe kamar su Amuka da Ingila sun sanya baki ba.

Comrade Frank ya yi kira ga kasashen duniya da su yi watsi da shugabancin Najeriya da shugabannin jam’iyyar APC mai mulki sannan su taimaka wajen wanzar da damokradiya a Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta gargadi kasashen waje da kada su yi mata katsalandar a harkokin Najeriya cewa tana da karfin gudanar da tsarin zaben kasar.

Da baka zama Shugaban kasa ba idan ba don US, da UK ba – Tsohon jigon APC ga Buhari

Da baka zama Shugaban kasa ba idan ba don US, da UK ba – Tsohon jigon APC ga Buhari
Source: Twitter

A wani jawabi da aka aike wa Legit.ng a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu, Comrade Frank ya bayyana furucin fadar Shugaban kasar a matsayin “wani sako daga teburin wani batulu.”

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Arewa ta marawa Buhari baya akan dakatar da Shugaban alkalan Najeriya

A cewarsa, da Buhari bai zamo Shugaban kasa ba a yau idan ba don kasashen duniya sun sanya baki a 2015 ba don tabbatar da gwamnatin wancan lokacin na Goodluck Jonathan ta gudanar da zabe na gaskiya da amana.

Yace abun mamaki ne cewa Buhari da ya yaba ma kokarin UK, US da sauran kasashen duniya akan zamowarsa Shugaban kasa a 2015 shine kuma a yanzu yake neman kada kasashen sun shigo lamuran kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel