Zan duba yiwuwar yafewa barayin Najeriya idan na ci zabe - Atiku

Zan duba yiwuwar yafewa barayin Najeriya idan na ci zabe - Atiku

Dan takarar shugabancin kasar Najeriya a jam'iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar yace yana tunanin watakila idan ya lashe zaben da za'a gudanar nan da 'yan kwanaki zai yafewa dukkan wadanda suka taba sace dukiyar kasar nan.

Atiku Abubakar din ya bayyana cewa zai yafe masu ne a bisa sharadin cewa za su maido dukkan abunda suka sata sannan kuma su zuba su a cikin kasar Najeriya domin habaka tattalin arzikin kasar.

Zan duba yiwuwar yafewa barayin Najeriya idan na ci zabe - Atiku

Zan duba yiwuwar yafewa barayin Najeriya idan na ci zabe - Atiku
Source: Twitter

KU KARANTA: Wasu fitattun 'yan Najeriya 2 sun fadawa Buhari gaskiya

Legit.ng Hausa ta samu cewa Atiku Abubakar wanda ke zaman tsohon mataimakin shugaban kasa yayi wannan bayanin ne lokacin da yake bayar da ansa a tattaunawar da yayi kai tsaye a wani shiri da 'yar jarida Kadaria Ahmed ta jagoranta.

Atiku wamda kuma ya samu rakiyar mataimakin sa da suke takara tare kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi yace yana kyawawan tsare-tsaren fitar da 'yan Najeriya miliyan 50 daga cikin matsanancin talauci.

A wani labarin kuma An samu wata 'yar karamar dirama ranar Talata da ta gabata a garin Owerri na jihar Imo wajen zabayen gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Muhammadu Buhari.

Mun samu cewa dai kawuna sun rabu ne biyo bayan sabanin da aka samu saboda rikicin da yanzu haka ke tsakanin uwar jam'iyyar ta APC a mataki na tarayya karkashin jagorancin Kwamared Adams Oshiomhole da kuma gwamnan jihar, Cif Rochas Okorocha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel