Ba zan daina yaki da rashawa ba – Buhari

Ba zan daina yaki da rashawa ba – Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin cigaba da yaki da rashawa matukar aka zabe shi a karo na biyu

- Shugaban yace zai yi amfani da fasahar mutanen kasar nan da albarkatun da ta mallaka don samuwar jin dadin mutane

- Yace ya tabbatar da shirye shiryen da yayi yakin neman zabe dasu a 2015

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin cigaba da yaki da rashawa matukar aka zabe shi a zaben 16 ga watan Fabrairu 2019.

Buhari yayi alkawarin ne yayin da yayi jawabi ga taron magoya bayan shi da suka shakare filin wasa na Pa Oruta Ngele dake Abakaliki a ranar laraba yayin kamfen din shi.

Ba zan daina yaki da rashawa ba – Buhari

Ba zan daina yaki da rashawa ba – Buhari
Source: Facebook

Yace maida hankalin da gwamnatin shi tayi wajen saitawa da gyara kasar akan almundana tana nan ba gudu ba ja da baya.

Buhari yace yaki da rashawa ba abu mai sauki bane, amma mulkin shi ba zai ja baya ba akan gwagwarmayar.

"Muna mummunan yaki da rashawa kuma wannan jan aiki ne amma kuma muna kokari don kawo gyara a bangaren yan sanda da shari'a. Idan muka zabi mutane su wakilce mu ofisoshi wadanda basu da mota ko gidaje, a cikin shekaru biyu kawai sai su mallaki mota, gina gidaje a Abuja, turai da Amurka. Idan muka binciko su, mu kama su, mu kaisu kotu tare da gurfanar dasu, muna fatan kuma za a yanke musu hukunci.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kwamishinan Yobe ya ajiye aiki domin zama mataimakin gwamna

"Abu mai muhimmanci da zan tabbatar muku shine ni shugaban kasa a yau ban taba kaiwa matakin da zan ci amanar yardar ku ba. Nayi gwamna a arewa maso gabas wacce yanzu aka maida jihohi shida, ministan man fetur na fiye da shekaru 3 kuma tsohon shugaban kasa. An kama ni, an kulle kuma anyi bincike akaina amma ba a samu komai na rashin gaskiya ba. A don haka ne zamu tsaya tare da kawar da duk abinda ya zai zamo barazana akan cigaban kasar nan saboda ubangiji ya bamu mutane da kuma ma'adanai."

"Idan kuka zabe ni a Karo na biyi, zan tabbatar da cewa nayi amfani da mutane da kuma ma'adanan da ubangiji ya bamu don maida rayuwar mu ta jin dadi da ta yayanmu," inji shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel