Kungiyar Arewa ta marawa Buhari baya akan dakatar da Shugaban alkalan Najeriya

Kungiyar Arewa ta marawa Buhari baya akan dakatar da Shugaban alkalan Najeriya

- Arewa Consultative Forum (ACF) ta mara wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya akan dakatar da shugaban alkalan Najeriya, Justis Walter Onnoghen

- Kungiyar ta yi kira ga hukumomin doka da su jajirce akan aikinsu cikin kwarewa da gasiya domin guje ma haifar da rigingimu a karshe

- ACF tace Najeriya ba za ta bunkasa ba da kaiwa inda take mafarkin zuwa har sai an koyi daraja doka da kuma aiki dasu yadda ya kamata

Kwamitin amintattu na kungiyar arewa wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta mara wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya akan dakatar da shugaban alkalan Najeriya, Justis Walter Onnoghen.

Kungiyar ta ACF ta bayyana hakan a wani taron jama’a karkashin shugabanta Alhaji Adamu Fika a Kaduna.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne dai ya dakatar da Onnoghen bayan an zarge shi da kin bayyana ainahin kadarorin da ya mallaka.

Kungiyar Arewa ta marawa Buhari baya akan dakatar da Shugaban alkalan Najeriya

Kungiyar Arewa ta marawa Buhari baya akan dakatar da Shugaban alkalan Najeriya
Source: UGC

A wani jawabi dauke da sa hannun sakatare janar na kungiyar, Mista Anthony Sani, yace an kawo cewa Justis Onnoghen ya fada ma masu bincike cewa dalilinsa na rashin kaddamar da wadannan kadarorin mantuwa ne.

Kungiyar tace bayan gano wadannan kadarori, sai kotun CCB ta tura lamarin ga kotu sauraron kararraki na da’ar ma’aikata wana tayi umurnin dakatar da Shugaban alkalan domin ayi hukunci na gaskiya.

Sai dai wannan mataki da kotun CCT ta dauka ya tunzura faruwar rigin-gimu da yawa.

KU KARANTA KUMA: Sarakunan gargajiya a Ebonyi sun marawa Buhari baya

ACF tace: “Mun yi matukar danasani da gudanarwar ustis Onnghen, musamman rashin komawarsa gefe sannan ya bari doka ta bi ka’idojinta cewa ya nuna cewa ya fi son kansa fiye da bangaren shari’a da kasar."

Kungiyar ta yi kira ga hukumomin doka da su jajirce akan aikinsu cikin kwarewa da gasiya domin guje ma haifar da rigingimu a karshe, cewa Najeriya ba za ta bunkasa ba da kaiwa inda take mafarkin zuwa har sai an koyi daraja doka da kuma aiki dasu yadda ya kamata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel