Mu kungiyar addini ne ba kungiyar ‘Yan siyasa ba – CAN ta ja-kunnen PDP

Mu kungiyar addini ne ba kungiyar ‘Yan siyasa ba – CAN ta ja-kunnen PDP

Mun samu labari daga wata jaridar kasar nan cewa ana can ana ta maidawa juna kalamai tsakanin Kungiyar CAN ta Kiristocin Najeriya da kuma babbar jam’iyyar hamayya watau PDP a game da zaben 2019.

Mu kungiyar addini ne ba kungiyar ‘Yan siyasa ba – CAN ta ja-kunnen PDP

Babban kungiyar addinin Kirista ta ki marawa ‘dan PDP baya
Source: Depositphotos

Kamar yadda labari ya zo mana, a daidai lokacin da ake shirin babban zaben shugaban kasa da gwamnoni da kuma majalisa a Najeriya. ce-ce-ku-ce ya barke ne tsakanin jam’iyyar PDP ta jihar Nasarawa da kuma kungiyar CAN.

PDP ta soki wani shugaban Kiristoci na CAN na jihar Nasarawa a dalilin kin yin na’am da mubaya’ar da manyan sa su kayi wa ‘Dan takarar jam’iyyar adawar. PDP tace shugaban CAN na jihar ya maida kungiyar tamkar mallakar sa.

Jam’iyyar adawar ta zargi babban jami’in da ke rike da kungiyar kiristocin ta jihar Nasarawa da nuna rashin goyon baya ga ‘yan takarar ta na zaben 2019 duk da cewa jagororin CAN na yankin Arewacin kasar kaf sun mara masu baya.

KU KARANTA: Idan na mutu a kama Buhari inji wani Gwamnan PDP

Manyan PDP sun nemi wani babban Shehi mai suna Joseph George Masin da ya sa baki a lamarin wajen ganin reshen CAN ta jihar Nasarawa ta tofawa ‘yan takaran ta albarka. Shugaban PDP na Nasarawa, Francis Orogu ya bayyana wannan.

Francis Orogu yace manyan CAN duk sun yi na’am da takarar Honarabul Davematics David E. Ombugadu sai dai bangaren kungiyar addinin na jihar Nasarawa ne kurum su ka ki sa wa takarar ‘dan PDP din albarka domin su samu nasara.

Kungiyar ta CAN dai ta kara jaddawa PDP cewa addini ne a gaban su ba wai tsaida hannun masu neman kujerar siyasa ko kuma ba su tabarruki ba. Yanzu dai saura ‘yan kwanaki a soma babban zabe a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel