Wasu Lauyoyi sun yi watsi da umarnin NBA na kauracewa kotu na kwana 2

Wasu Lauyoyi sun yi watsi da umarnin NBA na kauracewa kotu na kwana 2

Mun ji labari cewa Lauyoyin da ake da su a Najeriya sun samu kan-su cikin wani rabuwar kai a dalilin dakatar da Alkalin Alkalai da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a makon jiya da ya wuce.

Wasu Lauyoyi sun yi watsi da umarnin NBA na kauracewa kotu na kwana 2

Wasu sun bijirewa umarnin NBA bayan an dakatar da Alkalin Alkalai
Source: Twitter

Manyan Lauyoyin kasar nan sun shiga cikin wani hali na sabani game da matakin da za a dauka bayan da shugaban kasa ya murtike fuska ya nada wani sabon Alkalin Alkalai ba tare da jiran umarni daga majalisar shari’a ba.

Kan Kungiyar NBA ta Lauyoyi ya rabu biyu inda wasu su kayi wani gajeren yajin aiki domin yin bore a sakamakon dakatar da Walter Onnoghen da aka yi daga kujerar shugaban Alkalai, yayin da wasu kuma su ka ki yin biyayya.

KU KARANTA: Matasa sun yi wa shugaban kungiyar lauyoyi duka a jihar Ribas

Lauyoyin Najeriya da ke reshen NBA sun bada umarni a farkon makon na cewa Lauyoyi su kauracewa shiga kotu domin nuna fushi da nuna rashin amanna da taba babban Alkalin Najeriya da aka yi a Ranar Juma’ar da ta wuce.

Sai dai kamar yadda mu ka samu labari, wasu Lauyoyi sun yi watsi da wannan kira da uwar kungiyar NBA tayi inda su ka cigaba da halartar zaman kotu a daidai lokacin da ake kira ayi wa gwamnatin Najeriya bore na kwana 2.

A jihohi irin su Yobe dai manema labarai sun ce an yi zama a manyan kotun tarayya duk da wannan umarni da NBA ta bada. Shugaban NBA na jihar yayi kira ga Lauyoyin da ke Yobe cewa su yi watsi da wannan umarni da aka bada a baya.

KU KARANTA: Abin da ya sa mu ka dakatar da Alkalin Alkalai - Gwamnatin tarayya

A irin su jihar Kaduna, dai ba shakka Lauyoyi da dama sun kauracewa kotu inda aka ce an hangi manyan dakunan kotu wayam babu kowa a cikin su. Masu kare jama’a a Kaduna sun dauki wannan mataki da uwar kungiyar NBA ta bada.

A Garin Abuja dai mafi yawan Lauyoyi ba su je aiki ba, yayin da a Legas kuwa, an samu rabuwar kai, inda wasu Lauyoyi su ka fita aiki yayin da wasu su kayi gum. Sai dai a Jigawa, Lauyoyi sun watsawa NBA kasa a idanu ta yin bore ga umarnin ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel