Akwai yiwuwar wasu jam'iyyun siyasa su kauracewa zaben 2019 - NCP

Akwai yiwuwar wasu jam'iyyun siyasa su kauracewa zaben 2019 - NCP

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar National Conscience Party (NCP), Dr. Yunusa Tanko ya ce akwai yiwuwar wasu jam'iyyu za su kauracewa zaben 2019 saboda barazanar da gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ke yi.

Tanko wanda tsohon shugaba ne na IPAC, ya shaidawa Daily Trust yau a Abuja cewa gwamnatin jam'iyyar APC bata nuna alamun cewa za ta gudanar da sahihiyar zabe ba a shekarar 2019.

Ya ce ana tauye hakkin wasu 'yan kasa a halin yanzu.

Dr Tanko wadda har ila yau shine Ciyaman din jam'iyyar NCP na kasa ya ce baya ga kokarin sanyaya gwiwan jam'iyyun adawa gabanin zaben na 2019, jam'iyyar ta APC tana yiwa shugabanin jam'iyyun barazana.

Akwai yiwuwar wasu jam'iyyun siyasa su kauracewa zaben 2019

Akwai yiwuwar wasu jam'iyyun siyasa su kauracewa zaben 2019
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure

"Baya ga barazana, gwamnati mai ci yanzu tana saka tsoro a zukatan abokan hammaya da suke kokarin yin magana akan abubuwan da ta ke aikatawa.

"Akwai yiwuwar wasu jam'iyyun siyasa za su kauracewa zabe muddin aka cigaba da irin wannan karya dokokin ba tare da daukan mataki ba. Kawai za su zabi wadanda suke so ne amma ba zabe ba."

Ya ce, "Na samu labarin cewa an garkame wani mai rajin kare hakkin bil adama, Deji Adeyanju a kurkukun jihar Kano na kusan kwanaki 50. Na san cewa Deji yana daya daga cikin masu sukar gwamnati mai ci yanzu.

"A cikin 'yan makonnin nan, an rika kama shi ana gurafanar da shi a gaban kotun Majistare. A matsayina na dan gwagwarmaya mai rajin kare hakkin bil-adama, na san abu ne mai wuya tunkarar gwamnati da ke mulki.

"Amma wadanda ke mulki su tuna cewar a baya suma suna daga cikin masu sukar gwamnati da ke mulki kuma ba a hannu su bayyana ra'ayoyinsu ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel