Dakatar da Onnoghen: Matasa sun yiwa shugaban kungiyar lauyoyi duka a jihar Ribas

Dakatar da Onnoghen: Matasa sun yiwa shugaban kungiyar lauyoyi duka a jihar Ribas

Wasu gungun matasa da ake kyautata zaton 'yan bangan siyasa ne sun yiwa shugaban Kungiyar Lauyoyi na Kasa NBA na Fatakwal, Sylvester Adaka duka.

Lamarin ya faru ne a kotun daukaka kara da ke Fatakwal a jihar Rivers a ranar Laraba.

Rikicin ya samo asali ne yayin da wasu lauyoyi karkashin jagorancin Adaka suka ziyarci kotun da Justice A.A. Gumel ke shari'a kuma suka bukaci ya dage shari'ar saboda zanga-zangar da NBA keyi a kan dakatar da Walter Onnoghen a matsayin Alkalin Alkalai.

Dakatar da Onnoghen: Matasa sun lakadawa shugaban kungiyar lauyoyi duka a Ribas

Dakatar da Onnoghen: Matasa sun lakadawa shugaban kungiyar lauyoyi duka a Ribas
Source: Twitter

A bangarensa, Gumel ya gargadi lauyoyin kada su kawo rudani a kotu inda ya ce gudanar da zanga-zanga da yunkurin hana zaman kotu da lauyoyin ke yunkurin rashin da'a ne ga kotu.

DUBA WANNAN: Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure

Alkalin ya shaida musu cewar zai karbi wasu bayanai ne kawai amma ba zai saurari shari'a ba a ranar.

Sai dai lauyoyin ba su gamsu da wannan bayanin na alkalin ba wadda hakan ba yiwa wasu daga cikin 'yan bangan dadi ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa wasu daga cikin 'yan bangan sun kaiwa ciyaman din NBA da wasu lauyoyi hari inda suka nemi a cigaba da sauraron shari'a a kotun.

Tonye Cole na jam'iyyar APC da ke kotun ya yi tir da abinda ya faru.

Hakazalika, tsohon Ciyaman din NBA, reshen Fatakwal, Dennis Okwakpam ya bayyana rashin jin dadinsa a kan abinda ya faru a kotun daukaka karar.

Okwakpam ya ce, "Muna ciki mafi munin lokuta a wannan kasar, mutanen da suka san doka suna jefa siyasa a cikin dukkan harkokin kasa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel