Dalilin da yasa na ce masoyana su zabi yan takarar da suke so - Buhari

Dalilin da yasa na ce masoyana su zabi yan takarar da suke so - Buhari

- Shugaban kasa Buhari ya yi bayani akana dalilinsa na cewa masoyansa su zabi dan takarar da sukeso

- Ba iya yan jam'iyar APC ne suke goyon bayan shugaban kasar ba

- Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya musanta zargin da akeyi na cewar Buhari baya goyon bayan yan jam'iyar sa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace magoya bayan sa su zabi dan takarar da suke so kada suyi la'akari da jam'iya. Buhari ya fadi hakan ne a lokacin ziyarar yakin neman zabe da ya kai garin Imo da dake kudancin kasar nan.

Buhari ya fadi hakan ne a ranar talatar da ta gabata inda yace shi fa ba lallai sai sun zabi sak ba, su zabi duk Wanda ya fi kwanta musu a rai.

A jihar ta Imo dai ana fuskantar kace nace a harkar siyasar su sakamakon tsayar da Hope Uzodinma a matsayin dan takarar gwamna sai kuma zabin gwamna Rochas okorocha Wanda dan jamiyar Action Alliance ne wato Uche Nwosu.

Dalilin da yasa na ce masoyana su zabi yan takarar da suke so - Buhari

Dalilin da yasa na ce masoyana su zabi yan takarar da suke so - Buhari
Source: Facebook

Garba Shehu wanda shine me magana da yawun bakin shugaba buhari ya bayyana wa manema labarai cewa dalilin da yasa shugaba Buhari yace kowa ya zabi wanda yakeso shine duba da yadda a yakin neman zaben ba iya magoya bayan Buhari bane suka taru, harda yan wasu jam'iyun da suka hada kai domin marawa buhari baya a babban zabe me zuwa.

KU KARANTA KUMA: Sarakunan gargajiya a Ebonyi sun marawa Buhari baya

Wannan shine dalilin da yasa Buharin yace ba dole sai anyi sak ba.

Kakakin shugaban kasar ya musanta zargin da akeyi na cewar Buhari baya goyon bayan yan jam'iyar sa, saidai yace Buhari ya nuna jin dadin sa na ganin yan wasu jam'iyun suna goyon bayan sa shine yasa yace su zabi duk dan takarar da suka fi ganin cancantar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel