Hotuna: Gabanin zuwan Buhari Kano gobe, gwamna Ganduje ya je yawon duba kammalallun ayyuka biyu da Buhari zai kaddamar a Kano

Hotuna: Gabanin zuwan Buhari Kano gobe, gwamna Ganduje ya je yawon duba kammalallun ayyuka biyu da Buhari zai kaddamar a Kano

A yayin da rahotanni ke ci gaba da yaduwa sakamakon ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai jihar Kano a gobe Alhamis, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya shirya tsaf domin tarbar tawagar fadar shugaban kasa.

Daga cikin shirye-shiryen da yayi, gwamnan ya fita zagayen duba ayyukan ginin sabbin tituna biyu da shugaba Buhari zai kaddamar a kafin gabatar da yakin neman zabensa a jihar Kano.

Hadimin gwamnan kan sabbin kafafe yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana ayyukan biyu da shugaban kasan zai kaddamar inda yace:

"Ayyuka biyu da shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar sune:

1. Titin kasa dake Kofar Ruwa

2. Titin sama da ke hayar Murtala Muhammad Highway"

Ya kara da cewa wadannan ayyuka biyu shugaba Buhari ya zabi kaddamarwa cikin guda shida da gwamnatin jihar ta gabatar masa ya zaba.

Hadimin shugaba Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmed, ya jaddada cewa shugaba Buhari zai tafi jihar Kano gobe bayan ya fasa zuwa a ranan Lahadin da ya gabata.

KU KARANTA: Kungiyar magoya baya ta shirya yiwa Buhari gagarumar tarba a Kano

Kalli hotunan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel