Sarakunan gargajiya a Ebonyi sun marawa Buhari baya

Sarakunan gargajiya a Ebonyi sun marawa Buhari baya

- Sarakunan gargajiya a Ebonyi sun mara wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a kudirinsa na neman tazarce

- Sun bayar da wannan tabbacin ne a lokacin wani tattaunawa tare da Shugaban kasar a gidan gwamnatin jihar da ke Abakaliki

- Shugaban majalisar sarakunan, Eze Charles Mkpuma, yace sun lamuncewa Shugaban kasar ne saboda alakar da ke tsakanin Shugaban kasar da gwamna David Umahi

Kamar takwarorinsu na jihar Abia, sarakunan gargajiya a Ebonyi a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu sun mara wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari baya a kudirinsa na neman tazarce.

Sarakunan sun kuma yanke shawarar tabbatar da nasarar shugaba Buhari a zaben ranar 16 ga watan Fabarairu.

Sun bayar da wannan tabbacin ne a lokacin wani tattaunawa tare da Shugaban kasar a gidan gwamnatin jihar da ke Abakaliki.

Sarakunan gargajiya a Ebonyi sun marawa Buhari baya

Sarakunan gargajiya a Ebonyi sun marawa Buhari baya
Source: Facebook

Shugaban majalisar sarakunan, Eze Charles Mkpuma, yace sun lamuncewa Shugaban kasar ne saboda alakar da ke tsakanin Shugaban kasar da gwamna David Umahi.

KU KARANTA KUMA: Manyan dalilai 3 da suka sanya ni goyon bayan shugabancin Atiku - Obasanjo

Mkpuma yace Buhari ya cancanci kuri’unsu duk da banbancin jam’iyya sannan ya yaba ma jajircewarsa waen magance rashin tsaro a kasar da kuma yaki da yake yi da cin hanci da rashawa.

Sun bayyana cewa wannan kokarin zai sa Shugaban kasar ya samu kuri’u da dama a ranar zabe wanda za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Sarakunan sun kuma nuna goyon bayansu ga kudirin tazarcen gwamna Umahi cewa suna farin ciki da shugabancinsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel