PDP ta yi babban rashi: Tsohon shugaban NDDC, mutane 2000 sun koma APC a Akwa Ibom

PDP ta yi babban rashi: Tsohon shugaban NDDC, mutane 2000 sun koma APC a Akwa Ibom

Dubunnan mutanen na cigaba da sauye-sauyen sheka tsakanin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC) a jihar Akwa Ibom yayinda ake gab da fuskantar zaben shugaban kasa, gwamnoni da yan majalisa a watan gobe.

Jam'iyya APC ta samu gagarumin karuwa a jihar inda wani tsohon kwamishanan hukumar cigaba yankin Neja Delta NNDC, Mista Etim Inyang, tare da mabiyansa 2000 suka fita daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Mista Inyang, wanda dan tsohon kwamishanan yan sandan ne, Marigayi Cif Etim Inyang, ya jagoranci ayarin masu sauya shekan a taron yakin neman zabe a karamar hukumar Mbo na jihar.

Yayinda yake jawabi ga jama'an da ke wajen taro, Inyang ya bayyana cewa ya sauya sheka ne saboda marawa Obong Nsima Ekera bayan wajen samun nasara a zaben gwamnan jihar da zai gudana a watan Maris.

Yace: "Bari inyi aron kalma daga cikin littafin Injila inda Paul yace ba shi jin kunyan bin shiriyar annabi Isa. Ba na jin kunyan bin Obong Nsima Ekere daga zuciyata saboda shi kai kai mu ga cigaba."

Ya tabbatarwa Ekere cewa zai lashe kuri'un Mbo 51,112.

KU KARANTA: Mutan jihar Ebonyi sun yiwa Buhari kyakkyawan tarba (Hotuna da Bidiyo)

A bangare guda, mun kawo muku rahoton cewa NDLEA ta jihar Akwa Ibom a ranar Monday tace ta kama mutane 120 da ake zargi tare da miyagun kwayoyi a samamen shirye shiryen zabe da sukayi tsakanin Satumba 2018 da Janairu 2019.

Kwamandan jihar na NDLEA, Mr Mohammed Sokoto, ya bayyana hakan yayin jawabi ga manema labarai akan aiyukan cibiyar a Uyo a ranar talata.

Sokoto yace a lokacin, ofishin su ya kwace kilogram 51 na cannabis, gram 250 na wuiwi, gram 17 na hodar iblis da gram 500 na tramadol, diezepam da polypro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel