Sojojin Najeriya sun kashe yan ta’adda 4 a wata karanbatta a Borno

Sojojin Najeriya sun kashe yan ta’adda 4 a wata karanbatta a Borno

Dakarun rundunar Sojojin Najeriya sun samu galaba akan wasu gungun mayakan rundunar ta’addanci ta Boko Haram a yayin wata dauki ba dadi da suka yi da juna a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu a jahar Borno.

Legit.ng ta ruwaito Sojojin sun yi wannan arangama da mayakan Boko Haram ne da misalin karfe 9:30 na safiyar Laraba yayin da suke gudanar da aikin sintiri akan hanyar Gwoza zuwa Yemteke, a lokacin suka yi kicibus da gungun yan ta’addan.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mai magana da yawun gwamnan Taraba

Sojojin Najeriya sun kashe yan ta’adda 4 a wata karanbatta a Borno

Boko Haram
Source: Facebook

Sojojin da suka fito daga bataliya ta 192 basu nuna tsoro ko yin kasa a gwiwa ba, nan take suka ce da wa Allah ya hadamu in ba ku ba, suka shiga bude musu wuta, suna kara dannasu, tare da yin kwance kwance irin na dabarun Sojoji a fagen yaki.

Sojojin basu tsagaita wuta ba har sai da suka cimma mayakan yan ta’addan, inda suka kashe mutane hudu daga cikinsu, yayin da sauran suka ce kafa mai na ci ban baki ba?, suka ranta ana kare dauke da raunukan harsashi da suka samu a sakamakon artabun.

Bayan kura ta lafa Sojojin Najeriya sun gano wasu bindigu kirar AK 47 da mayakan Boko Haram suka jefar, da kuma alburusai da dama, mallakin yan ta’addan da Sojoji suka halaka.

Sojojin Najeriya sun kashe yan ta’adda 4 a wata karanbatta a Borno

Boko Haram
Source: Facebook

A wani labarin kuma, Dakarun rundunar Sojoji ta Operation sharan daji dake aikin tabbatar da tsaro a tsakanin jihohon Katsina, Zamfara da Sakkwato sun halaka yan bindiga guda 21 a wani muhimmin samame da suka kai a sansanoninsu, sa’annan suka ceto mutane 89 dake hannunsu.

Mukaddashin kaakakin rundunar, Manjo Clement Abiade ne ya sanar da haka a ranar Talata 29 ga watan Janairu na shekarar 2019, inda yace Sojojin sun samu wannan nasara ce cikin sati daya kacal, inda suka kashe yan bindiga 21, suka kama wasu 17 da ransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel