Yanzu Yanzu: EFCC ta shigar da qara kan Babachir Lawal da mukarrabansa su 5

Yanzu Yanzu: EFCC ta shigar da qara kan Babachir Lawal da mukarrabansa su 5

- Hukumar EFCC ta sanya wasu tuhume-tuhume 10 akan tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Injiniya Babachir Lawal

- Ana tuhumarsa ne tare da Hamidu David Lawal; Sulaiman Abubakar; Apeh John Monday; Rholavision Engineering Limited da kuma Josmon Technologies Limited

- Dukkaninsu za su fuskanci shari’a a babbar kotun tarayya da ke babbar birnin tarayya

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tatalin arziki zagon kasa (EFCC)a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu ta sanya wasu tuhume-tuhume 10 akan tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Injiniya Babachir Lawal da wasu biyar.

Suran sune; Hamidu David Lawal; Sulaiman Abubakar; Apeh John Monday; Rholavision Engineering Limited da kuma Josmon Technologies Limited.

Dukkaninsu za su fuskanci shari’a a babbar kotun tarayya da ke babbar birnin tarayya, Abuja.

Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan Kungiyar HEDA mai zaman kan-ta, tayi kira ga gwamnatin tarayya tayi maza ta fara binciken tsohon Sakataren gwamnatin tarayyar watau Babachir David Lawal da kuma tsohon shugaban hukumar NIA na kasa Ayo Oke.

Yanzu Yanzu: EFCC ta shigar da qara kan Babachir Lawal da mukarrabansa su 5

Yanzu Yanzu: EFCC ta shigar da qara kan Babachir Lawal da mukarrabansa su 5
Source: UGC

HEDA ta yi barazanar maka gwamnatin Najeriya a kotu nan da kwanaki 30 idan har ba ta soma binciken Injiniya Babachir Lawal da Ayodele Oke ba. Kungiyar mai fafatukar ganin an gyara sha’anin mulki ta bayyana wannan ne jiya.

KU KARANTA KUMA: Manyan dalilai 3 da suka sanya ni goyon bayan shugabancin Atiku - Obasanjo

A wata wasika da shugaban kungiyar ya aikawa Ministan shari’a na kasa, ya yabawa yadda gwamnatin Buhari ta ke binciken Walter Onnoghen wanda yanzu an dakatar da shi daga matsayin Alkalin Alkalai saboda zargin da ke kan sa.

Kungiyar tace yadda aka gurfanar da CJN Walter Onnoghen, haka ya zama dole a taso keyar Babachir Lawal da Ayodele Oke wadanda aka kora daga mukamin su a gwamnatin nan bisa zargin aikata ba daidai ba a lokacin su na ofis.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel