Bukatar zuwa asbibitin kasar waje: Kotu ta watsa ma tsohon kaakakin PDP kasa a idanu

Bukatar zuwa asbibitin kasar waje: Kotu ta watsa ma tsohon kaakakin PDP kasa a idanu

Wata kotun daukaka kara ta yi fatali da bukatar da tsohon kaakakin jam’iyyar PDP, Olisa Metuh ya shigar gabanta yana neman ta bashi izinin fita daga Najeriya zuwa daya daga cikin manyan kasashen duniya domin ya samu ganin likita game da wata cuta dake damunsa.

Makasudin shigar da karar shine Olisa Metuh ya nemi kotun daukaka karar tayi watsi da hukuncin wata babbar kotun tarayya wanda ta fara hanashi zuwa ko ina a kasar waje da nufin zuwa duba lafiyarsa.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mai magana da yawun gwamnan Taraba

Bukatar zuwa asbibitin kasar waje: Kotu ta watsa ma tsohon kaakakin PDP kasa a idanu

Metuh
Source: UGC

Sai dai Metuh bai cimma bukatarsa ba, inda a maimakon kotun ta kawar da hukuncin babbar kotun, sai ma ta tabbatar da hukuncinta, inda tace bata ga dalilin da zai sa ta amince ma Metuh ya fita daga Najeriya da sunan neman lafiyarsa ba.

Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun ya bayyana dalilin da zai sa ba zai umarci hukumomin gwamnati su mika ma Metuh takardun tafiye tafiyensa ba, inda yace Metuh da lauyoyinsa sun raina ma kotun hankali ta hanyar rashin nuna wani gamsashen bayani dake nuni da irin cutar dake damunsa.

Haka zalika Alkalin kotun yace babu wata kwakkwaran shaida daga wani kwararren likita ko asibiti a ciki da wajen kasar nan da Metuh ko lauyoyinsa suka nuna ma kotun na cewa akwai bukatar ya tafi asibiti, don haka Alkalin ya watsa masa kasa a ido.

Shi dai Metuh a yanzu haka yana fuskantar tuhuma daga hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC akn zarginsa da dumbuza hannu tare da diban kasonsa daga kudi dala biliyan 21 dake jibge a ofishin tsohon mashawarcin shugaban kasa akan harkar tsaro Sambo Dasuki.

Da farkon shari’ar Metuh ya fara ma EFCC taurin kai, amma da yaga uwar bari, sai ya saki jiki, har ma yana yi musu magiya tare da faduwa a gaban kotu da sunan bashi da lafiya, wannan ne yasa hukumar take ganin tamkar yana neman hanyar sulalewa ne daga kasar da wannan bukata tashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel