Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mai magana da yawun gwamnan Taraba

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mai magana da yawun gwamnan Taraba

Wasu gungun miyagu masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da kaakakin gwamnan jahar Taraba Darius Ishaku, Hassan Mijinyawa a ranar Laraba, 30, ga watan Janairu a Jalingo, babban birnin jahar Taraba, inji rahoton Tribune.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun cika hannu da Hassan ne da safiyar yau yayin da yake tafiya zuwa ganawa da gwamnan jahar akan hanyar Bali Gashaka a cikin motar aiki tare da direbansa.

KU KARANTA; Sai yanzu muka san takamaimen adadin gangan danyen mai da muke fitarwa – Ministan Buhari

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mai magana da yawun gwamnan Taraba

Hassan Mijinyawa
Source: Facebook

Wata majiya ta bayyana cewa; “A yau aka sace shi yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa ganawa da gwamnan jahar Taraba Darius Ishaku, wanda yayi tafiya zuwa garin Gashaka tun a ranar Talata, gwamnan ne ya umarceshi ya kai masa wasu abubuwa daya manta a ofis.

“Da sanyin safiyar yau suka nufi garin Gashaka tare da direbansa, kwatsam sai muka ji matarsa ta kira mataimakin gwamnan jahar Taraba, Haruna Manu tana shaida masa cewa masu garkuwa da mutane sun kama mijinta.

“A cewar matar, yan bindigan sun tare motar mijinnata ne, inda suka daukeshi shi kadai ba tare da sun taba direban ba, daga bisani ne suka yi amfani da wayarsa wajen kiran matarsa, inda suka shaida mata halin da yake ciki.” Inji majiyar.

Shima mataimakin gwamnan jahar Taraba, Haruna Manu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace matar Mijinyawa ta kai masa ziyara har gida, inda ta shaida masa cewa yan bindiga da dama dauke da bindigar AK47 sun yi awon gaba da mijinta.

Sai dai Manu yayi kira ga jama’an jahar Taraba dasu kwantar da hankulansu, a cewarsa yanzu ba lokacin tayar da hankali bane, kamata yayi kowa ya shiga yi ma Hassan addu’ar Allah ya tseratar dashi tare da yi ma jahar gaba dayanta addua.

Kwamishinan Yansandan jahar Taraba, David Akinlemi ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai yace ba zai yi karin bayani ba har sai ya samu cikakken bayani daga bakin jami’an Yansandan daya tura wajen da aka ce lamarin ya faru.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel