Matafiya su hankalta: Ba a dasa Bom a jirgin Air Peace daga Abuja zuwa Legas ba - NAAF

Matafiya su hankalta: Ba a dasa Bom a jirgin Air Peace daga Abuja zuwa Legas ba - NAAF

- Hukumar FAAN ya bayyana cewa rade raden da ake yi na cewar an dasa Bom a cikin jirgin sama na Air Peace da ya tashi a safiyar yau daga Abuja zuwa Legas

- Hukumar ta ce fasinjan da ya yi wannan zargin na cewar an dasa Bomb a cikin jirgin, bayan gudanar da bincike, an gano yana dauke da ciwon tabin kwakwalwa

- Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa an samu rudani a cikin jirgin saman a safiyar ranar Laraba, bayan da wani fasinja ya yi zargin cewa akwai Bomb a cikin jirgin

A ranar Larabar nan, hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta kasa (FAAN) ya bayyana cewa rade raden da ake yi na cewar an dasa Bom a cikin jirgin sama na Air Peace da ya tashi a safiyar yau daga Abuja zuwa Legas.

Mrs Herietta Yakubu, babbar majanar harkokin kamfanonin kasuwa na hukumar FAAN, ta karyata jita jitar a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Laraba a Abuja.

Yakubu ta ce fasinjar da ya yi wannan zargin na cewar an dasa Bomb a cikin jirgin, bayan gudanar da bincike a kansa, an gano yana dauke da ciwon tabin kwakwalwa.

KARANTA WANNAN: Hattara 'yan Nigeria: Martaba da darajar Buhari da kuke gani dodo-rido ce - Obasanjo

Matafiya su hankalta: Ba a dasa Bom a jirgin Air Peace daga Abuja zuwa Legas ba - NAAF

Matafiya su hankalta: Ba a dasa Bom a jirgin Air Peace daga Abuja zuwa Legas ba - NAAF
Source: Twitter

Ta ce: "Biyo bayan wannan zargin karyar, jami'an tsaro na hukumar FAAN ta kwashe dukkanin fasinjoji daga jirgin, dama daukacin ma'aikata da kayan da ke a ciki, yayin da rundunar da ke lalata Bom ta gudanar da bincike a cikin jirgin, inda ta tabbatar da cewa zargin ba bu gaskiya a cikinsa.

"Bayan gudanar da kwakkwaran binciken kwakwaf a cikin jirgin, an sake kiran matafiya domin shiga cikin jirgin, inda aka kwashe su zuwa filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

"FAAN na son kara tabbatarwa matafiya da kuma dukkanin masu amfani da tashoshin jiragen sama cewa tashoshin kasar na cike da kulawa da tsaro daga dukkanin wani abu da ka iya kawo asarar rayuka ko dukiya.

"Kar jama'a su kasance cikin tsoro da fargaba, su gudanar da harkokinsu a cikin tashoshin jiragen," a cewar ta.

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa an samu rudani a cikin jirgin saman a safiyar ranar Laraba, bayan da wani fasinja ya yi zargin cewa akwai Bomb a cikin jirgin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel