Ba a taba kama ni da laifin rashawa ba - Buhari ya kaddamar

Ba a taba kama ni da laifin rashawa ba - Buhari ya kaddamar

- Shugaban kasa Buhari ya kaddamar da cewa a dukkanin mukaman da ya rike a kasar, ba a taba kama shi da laifin aikata rashawa ba

- Ya bayyana hakan ne a dakin taro na garin Abakaliki da ke jihar Ebonyi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da cewa a dukkanin mukaman da ya rike a kasar, ba a taba kama shi da laifin aikata rashawa ba.

Ya bayyana hakan ne a dakin taro na garin Abakaliki da ke jihar Ebonyi.

Buhari ya kasance tsohon Shugaban kasa na mulkin soja a shekarar 1983 zuwa 1985, ya kuma rike mukamin gwamnan jihar arewa maso yamma a 1975–1976, sannan yayi Shugaban Petroleum Trust Fund (PTF) a tsakanin 1994 zuwa 1995 sannan kuma a yanzu shine shugaban kasar Najeriya.

Ba a taba kama ni da laifin rashawa ba - Buhari ya kaddamar

Ba a taba kama ni da laifin rashawa ba - Buhari ya kaddamar
Source: Facebook

A halin da ake ciki, mun ji cewa, a yayin ci gaba da yawon shawagi da karade jihohi 36 na Najeriya domin girgiza magoya baya, a yau Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar da taron yakin neman zaben sa a birnin Abakaliki na jihar Ebonyi.

KU KARANTA KUMA: An sake soke zaman majalisar zartarwa na wannan makon

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, Shugaban kasa Buhari ya dira cikin karaji da kururuwar magoya baya da misali karfe 9.30 na safiyar yau Laraba a Barikin soji na Nkwegu da ke Abakaliki.

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya samu kyakkyawar tarba ta Kwamandun soji da kuma sauran jiga-jigai na jam'iyyar sa. Yayin amsa goron gayyata shugaba Buhari ya kuma garzaya fadar gwamnan jihar, Cif Dave Umahi domin sauke gajiyar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel