Hattara 'yan Nigeria: Martaba da darajar Buhari da kuke gani dodo-rido ce - Obasanjo

Hattara 'yan Nigeria: Martaba da darajar Buhari da kuke gani dodo-rido ce - Obasanjo

- Olusegun Obasanjo ya bada tabbacin cewa Alhaji Atiku Abubakar, shi ne zai lashe zaben shugaban kasa mai zuwa domin ya cire kasar daga cikinkuncin da take ciki

- Obasanjo ya ce martaba da darajar da jama'a ke kallo a jikin shugaban kasa Muhammadu Buhari dodo-rido ce

- Ya ce ya yafewa Atiku Abubakar akan dukkanin wasu laifuka da ya yi masa, yana mai cewa ya soke duk wata yarjejeniya ko taimakekeniya da ya kulla da Buhari a baya

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bada tabbacin cewa dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, shi ne zai lashe zaben shugaban kasa na ranar 16 ga watan Fabreru, saboda shine mutumin da ya dace ya cire kasar daga cikin halin kuncin da take ciki.

Da ya ke jawabi a ranar Laraba a wani taron lakca da aka shirya kan harkokin kasuwanci na Island Clube 2019 da ya gudana a birnin Legas, Obasanjo ya ce martaba da darajar da jama'a ke kallo a jikin shugaban kasa Muhammadu Buhari dodo-rido ce, yana mai cewa dukkanin matakan da shugaban kasar ke dauka na tabbatar da rashin dattakonsa.

Obasanjo ya ce ya yafewa Atiku Abubakar akan dukkanin wasu laifuka da ya yi masa, yana mai cewa ya soke duk wata yarjejeniya ko taimakekeniya da ya kulla da Buhari a baya.

Cikakken labarin yana zuwa...

KARANTA WANNAN: Wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar dokoki a APC sun tuntubi iyalinsa kan kudin fansa

Hattara 'yan Nigeria: Martaba da darajar Buhari da kuke gani dodo-rido ce - Obasanjo

Hattara 'yan Nigeria: Martaba da darajar Buhari da kuke gani dodo-rido ce - Obasanjo
Source: UGC

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta samu yanzu kuwa; Wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar dokoki na jamiyyar APC a mazabar Owan ta Yamma a jihar Edo, Michael Ohio-Ezomo, sun fara tattaunawa da iyalan dan majalisar, kwanaki hudu bayan yin garkuwa da shi.

Rahotannin sun nuna cewa masu garkuwar sun bukaci wasu makudan kudade da ba a bayyana yawansu ba daga hannun iyalin dan majalisar a matsayin kudin fansarsa.

Idan za a iya tunawa an shiga har cikin gidan Ohio-Ezom da ke garin Eme-Ora a safiyar ranar Alhamis, inda aka sace shi. A yayin sace shi, masu garkuwa da shi sun harbe wani dan sanda har lahira.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel