An sake soke zaman majalisar zartarwa na wannan makon

An sake soke zaman majalisar zartarwa na wannan makon

- An soke zaman majalisar zartarwa na mako da ya kamata ya gudana a yau Laraba, 30 ga watan Janairu

- Hakan ya biyo bayan kamfen din da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya je gudanarwa a jihohin Ebonyin da Cross Rive

- Wannan shine karo na biyu da ake soke zaman a cikin mako biyu

Rahotanni sun kawo cewa an soke zaman majalisar zartarwa na mako da ya kamata ya gudana a yau Laraba, 30 ga watan Janairu yayinda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja jirgin yakin neman zabansa zuwa jihohin Ebonyi da Cross River.

Wannan shine karo na biyu da ake soke zaman a makonni biyu a jere yayinda Shugaban kasa da mataimakinsa Yemi Osinbao suka mayar da hankali wajen kamfen din neman tazarce a zabe mai zuwa.

An sake soke zaman majalisar zartarwa na wannan makon

An sake soke zaman majalisar zartarwa na wannan makon
Source: Facebook

Idan har Shugaban kasa baya nan, mataimakin Shugaban kasar kan jagoranci zaman majalisar inda anan ne ake tattauna matsalolin asa da kuma amincewa da ayyukan kasar.

A makon da ya gabata, Shugaban kasar ya je jihohin Sokoto da Kebbi domin yin kamfen yayinda mataimakin Shugaban kasar kuma ya mayar da hankali ga kamfen dinsa na gida-gida don haka ba a gudanar da zaman ba.

KU KARANTA KUMA: Bara-gurbin da ke jam’iyya mai mulki duk yan PDP ne da suka sauya sheka – Dan majalisa na APC

A lokacin da aka kira kakakin Shugaban kasar, Femi Adesina yace babu wata doka da tace zai an gudanar da zaman majalisar a kowani mako.

Yace a lokacin gwamnatin shugaba Umaru Musa Yar’Adua, ana gudanar da zaman ne bayan makonni biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel