Yakin Zabe: Buhari ya ziyarci jihar Ebonyi

Yakin Zabe: Buhari ya ziyarci jihar Ebonyi

Za ku ji cewa, a yayin ci gaba da yawon shawagi da karade jihohi 36 na Najeriya domin girgiza magoya baya, a yau Laraba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar da taron yakin neman zaben sa a birnin Abakaliki na jihar Ebonyi.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, Shugaban kasa Buhari ya dira cikin karaji da kururuwar magoya baya da misali karfe 9.30 na safiyar yau Laraba a Barikin soji na Nkwegu da ke Abakaliki.

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya samu kyakkyawar tarba ta Kwamandun soji da kuma sauran jiga-jigai na jam'iyyar sa. Yayin amsa goron gayyata shugaba Buhari ya kuma garzaya fadar gwamnan jihar, Cif Dave Umahi domin sauke gajiyar sa.

Yakin Zabe: Buhari ya ziyarci jihar Ebonyi

Yakin Zabe: Buhari ya ziyarci jihar Ebonyi
Source: Facebook

Tawagar da ta take wa shugaban kasa Buhari baya ta hadar da shugaban jam'iyyar APC na kasa Kwamared Adams Oshiomhole, Ministan kwadago da aikace-aikace, Dakta Chris Ngige da kuma takwaran sa na ma'aikatar Sufuri da ya kasance jagoran tafiya, Cif Rotimi Amaechi.

KARANTA KUMA: Gwamna Okowa ya bayar da kyautar N2m ga wata jaririya da aka haifa yayin taron yakin zabe a jihar Delta

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an tsananta tsaro a jihar Ebonyi yayin taron yakin neman zaben shugaban kasa Buhari da aka gudanar a harabar filin wasanni na Pa Oruta Ngele da ke birnin Abakaliki.

Kazalika kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya kuma ruwaito cewa, magoya baya na Buhari da kuma jam'iyyar sa ta APC sun cika sun batse a filin wasannin domin nuna tsagwaran soyayyar da goyon bayan akidar tazarce yayin da babban zaben kasa ya karato.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel