Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC ya sauya sheka zuwa PDP

Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC ya sauya sheka zuwa PDP

- Mataimakin Shugaban jam’iyyar PDP, Samuel Ode-Oru tare da mambobin jam’iyyar sama da dubu shida suka koma PDP

- Hakazalika, jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ma ta hadu na nata rashin yayinda dan takararta na majalisar wakilai Paul Igwe ya koma PDP

- Ode-Oru yace nasarorin Gwamna Umahi a cikin kasa da shekaru hudu a mulki ne yasa shi yanke shawarar komawa PDP

Jam’iyyar All Progressive Congress party (APC) ta yi babban rashi a jihar Ebonyi inda mataimakin Shugaban jam’iyyar Samuel Ode-Oru tare da mambobin jam’iyyar sama da dubu shida suka koma PDP yan kwanaki kadan kafin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kamfe dinsa a jihar.

Hakazalika, jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ma ta hadu na nata rashin yayinda dan takararta na majalisar wakilai Paul Igwe ya koma PDP.

Ode-Oru da Igwe tare da daruruwan magoya bayansu sun sanar da sauya shekarsu a ganganmin jam’iyyar PDP a Ebiaji, kramar hukumar Ezza North da Ezzamgbo, karamar hukumar Ohaukwu da ke jihar Ebonyi.

Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC ya sauya sheka zuwa PDP

Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC ya sauya sheka zuwa PDP
Source: UGC

Yayinda yake sanar da sauya shekarsa, Ode-Oru yace nasarorin Gwamna Umahi a cikin kasa da shekaru hudu a mulki ne yasa shi yanke shawarar komawa PDP.

KU KARANTA KUMA: Bara-gurbin da ke jam’iyya mai mulki duk yan PDP ne da suka sauya sheka – Dan majalisa na APC

Ya kuma yaga katin kasancewara dan APC a bainar jama’a inda a take aka mika masa lema domin nuna cewar ya samu karbuwa a PDP.

Gwamna David Umahi wanda ya kasance a wajen gangamin ya jinjina wa wadanda suka sauya shekar zuwa jam’iyyarsa.

A wani lamari na daban, mun ji cewa cewa Sanatan Kaduna ta tsakiya watau Kwamared Shehu Sani ya bayyana cewa nan gaba kadan sai gwamna Malam Nasir El-Rufai ya juyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya.

Sanata Shehu Sani ya bayyana wannan ne a lokacin da yayi hira da Osasu Igbinedion a cikin shirin nan na Osasu Show. Sanatan yace da zarar Buhari ya bar kan kujerar mulki, Nasir El-Rufai zai juya masa baya kamar yadda ya saba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel