Wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar dokoki a APC sun tuntubi iyalinsa kan kudin fansa

Wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar dokoki a APC sun tuntubi iyalinsa kan kudin fansa

- Wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar dokoki a jihar Edo sun tuntubi iyalinsa kan kudin fansa, wanda ba a bayyana adadin yawan kudin da suka bukata ba

- Rahotanni sun bayyana cewa wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar, sun kira iyalansa na a wayar tarho, kwanaki hudu bayan sace shi

- Idan za a iya tunawa an shiga har cikin gidan Ohio-Ezom a safiyar ranar Alhamis, inda aka sace shi. A yayin sace shi, sun harbe wani dan sanda har lahira

Rahotanni sun bayyana cewa, wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar dokoki na jamiyyar APC a mazabar Owan ta Yamma a jihar Edo, Michael Ohio-Ezomo, sun fara tattaunawa da iyalan dan majalisar, kwanaki hudu bayan yin garkuwa da shi.

Rahotannin sun nuna cewa masu garkuwar sun bukaci wasu makudan kudade da ba a bayyana yawansu ba daga hannun iyalin dan majalisar a matsayin kudin fansarsa.

KARANTA WANNAN: Zaben 2019: Manyan shuwagabannin jam'iyyun siyasa sun sauya sheka zuwa APC a Adamawa

Wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar dokoki a APC sun tuntubi iyalinsa kan kudin fansa

Wadanda suka yi garkuwa da dan majalisar dokoki a APC sun tuntubi iyalinsa kan kudin fansa
Source: Twitter

Idan za a iya tunawa an shiga har cikin gidan Ohio-Ezom da ke garin Eme-Ora a safiyar ranar Alhamis, inda aka sace shi. A yayin sace shi, masu garkuwa da shi sun harbe wani dan sanda har lahira.‎

"Bayan zaman jira na kwanaki hudu, daga karshe wadanda suka yi garkuwa da shi sun kira iyalan domin tattaunawa da su. A jiya Talata suka kira, amma saboda tsaro ba zan iya fayyace adadin kudin da suka bukata ba, saboda gudun kar a samu cikas wajen sako dan uwan namu," a cewar wata majiya daga iyalan dan majalisar.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Hakeem Odumosu a yayin tabbatar da lamarin garkuwa da dsn majalisar, ya ce yana zargin wani na gida da hada baki da masu garkuwa da dan majalisar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel