Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar Jastis Walter Onnoghen

Yanzu-yanzu: Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar Jastis Walter Onnoghen

Labarin da ke shigo mana yanzunan na nuna cewa kotun daukaka kara ta yi watsi da karar da korarren shugaban alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen, ya shigar domin tsagaita gurfanarsa a kotun hukunta ma'aikatan gwamnati wato CCT.

Alkalin kotun daukaka karan, Jastis Abdul Aboki, ya yi watsi da karan ne saboda sashe na 306 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya haramta tsagaita gurfanar wani mutum idan ya aikata babban laifi.

Kotun a ranan Laraba tace bukatar da Onnoghen ya kawo kwanko ne saboda babu wani dalili a shari'a da zai amsa irin wannan bukata.

Game da cewwar Alkalin, Lauyoyin Onnoghen sun kawo kuka kotun daukaka kara ne saboda a ranan 14 ga watan Junairu kotun CCT ta ki basu daman kalubalantar hallacin gurfanar da korarren shugaban Alkalai.

Ya dakatad da karan zuwa ranan 4 ga watan Febrairu, 2019.

KU KARANTA: Yadda mutan jihar Imo suka tarbi shugaba Buhari

A bangare guda, Lauyoyin Najeriya 25 sun shigar da shugaban Muhammadu Buhari babban kotun tarayya da ke zaune a birnin tarayya Abuja domin kalubalantar dakatad da shugaban Alkalai, Jastis Walter Onnoghen, da akayi ranan Juma'a.

Wannan kara ya biyo bayan shari'ar kotun hukunta ma'aikatan gwamnati wato CCT wacce ta bayyana da safe cewa ta daga zama sauraron zargin da ake yiwa Walter Onnoghen har sai ila ma shaa'a LLahu.

Lauyoyin da suka shigar da karan karkashin jagorancin , Mr Johnmary Jideobi, ya gabatar da maganganu biyu gaban kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel