Bara-gurbin da ke jam’iyya mai mulki duk yan PDP ne da suka sauya sheka – Dan majalisa na APC

Bara-gurbin da ke jam’iyya mai mulki duk yan PDP ne da suka sauya sheka – Dan majalisa na APC

- Wani mamba a majalisar wakilai daga jihar Edo, Johnson Agbonayinma, ya zargi mambobin PDP da suka dawo APC da zama bara-gurbin da ke bata yaki da rashawar Buhari

- Agbonayinma ya caccaki jam’iyyar PDP aan sukar dakatarwar da Buhari ya yiwa Shugaban alkalan Najeriya, Justice Walter Onnoghen

- Dan majalisar ya kalubalanci PDP da ta gabatar da wani mafita kan yadda za a yaki cin hanci da rashawa

Wani mamba a majalisar wakilai daga jihar Edo, Johnson Agbonayinma, ya yi ikirarin cewa wadanda suka sauya shekka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bara-gurbin jam’iyyar mai mulki a yanzu.

Agbonayinma wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, yace mambobin jam’iyyar adawa da suka dawo jam’iyyar mai mulki sun dawo ne da kudirin dakile yaki da rashawarar shugaba Buhari, jaridar Tribune ta ruwaito.

Bara-gurbin da ke jam’iyya mai mulki duk yan PDP ne da suka sauya sheka – Dan majalisa na APC

Bara-gurbin da ke jam’iyya mai mulki duk yan PDP ne da suka sauya sheka – Dan majalisa na APC
Source: Depositphotos

Jigon na APC ya caccaki jam’iyyar PDP aan sukar dakatarwar da Buhari ya yiwa Shugaban alkalan Najeriya, Justice Walter Onnoghen sannan ya kalubalanci jam’iyyar adawar da ta gabatar da wani mafita kan yadda za a yaki cin hanci da rashawa.

“Matsalar game da yakar barayi ne. PDP kan yi Magana ne kadai akan bin tsari idan ya shafi yaki da cin hanci da rashawa. Idan yan fashi da barayi suka sace arziki, abu mai Magana akan bin tsari. PDP ta gabatar da wani mafita kan yadda za a yaki rashawa tunda yakar rashawa ya zama laifi a PDP,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin sama ta lalata sansanin dabaru na Boko Haram a dajin Sambisa

A wani lamari na daban, mun ji cewa Sanatan Kaduna ta tsakiya watau Kwamared Shehu Sani ya bayyana cewa nan gaba kadan sai gwamna Malam Nasir El-Rufai ya juyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel