Kungiyar Ohanaeze ta Ndi-Igbo, ta dakatar da sakatarenta kan 'azarbabinsa'

Kungiyar Ohanaeze ta Ndi-Igbo, ta dakatar da sakatarenta kan 'azarbabinsa'

- Sakataren kungiyar yace sun yanke zabar Buhari

- Kwaitin da aka zaunar na gaggawa ya dakatar dashi

- Kabilar Igbo dai Atiku suke yi

Kungiyar Ohanaeze ta Ndi-Igbo, ta dakatar da sakatarenta kan 'azarbabinsa'

Kungiyar Ohanaeze ta Ndi-Igbo, ta dakatar da sakatarenta kan 'azarbabinsa'
Source: UGC

Kungiyar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo ta dakatar da sakataren kungiyar, Mr Uche Okwukwu saboda zargin shi da wakiltar kungiyar ta yanda bai dace ba.

A wata takarda da sakataren hulda da jama'a na kungiyar, Mr Uche Okpaga ya bawa manema labarai a ranar alhamis a Enugu yace an yanke shawarar ne bayan taron gaggawa.

GA WANNAN: NBA: An sami sabani a arewa, kan kiran ayi wa Kotuna tawaye a kaurace musu kan sauke na biyar a kasar nan

Daga cikin zunubbansa a cewar kungiyar ta Igbo zalla, tace ya ari bakin kungiyar yayi azarbabin cewa a zabi shugaba Buhari, kuma yana gogawa da dasawa da manyan 'yan APC, lamari da suka ce an ari bakinsu ne an ci musu albasa,

Ana yawan sa rai dai kungiyar PDP take yi, kuma musamman ganin Peter Obi na Anambara yana tikitin PDp na Atiku Abubakar, su kuwa yarabawa suna so Buhari ya zarce don ya basu suma suyi takwas.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel