Gwamna Okowa ya bayar da kyautar N2m ga wata jaririya da aka haifa yayin taron yakin zabe a jihar Delta

Gwamna Okowa ya bayar da kyautar N2m ga wata jaririya da aka haifa yayin taron yakin zabe a jihar Delta

Cikin iko na Mai Duka, mun samu cewa, an haife wata santaleliyar jaririya ana tsaka da taron yakin neman zaben kujerar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Delta. Hakan ya sanya gwamnan jihar Ifeanyi Okowa, ya yi abin bajinta da kyautatawa.

Da sanadin shafin jaridar Premium Times mun samu cewa, gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa, ya bayar da kyauta da kuma tukwicin Naira miliyan biyu ga wata jaririya da aka haife ana tsaka da taron yakin neman zaben gwamna na jam'iyyar PDP.

Gwamna Ifeanyi Okowa

Gwamna Ifeanyi Okowa
Source: Depositphotos

Rabo da sai ya tsaga ya kan tabbata ya sanya gwamna Okowa ya bayar da sanarwar wannan gagarumar kyautata ga jaririyar da aka haifa a harabar taron yakin neman zabe na babbar jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Delta.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an haife jaririyar ne a ranar Talatar da ta gabata yayin yakin neman zabe da aka gudanar a karamar hukumar Ethiope ta Gabas tare da taimakon ma'aikatan lafiya na gwamnatin jihar da suka kasance a farfajiyar babban taron.

KARANTA KUMA: 2019: Ya zama wajibi Yarbawa su zabi Buhari - Afenifere

Gwamna Okowa ya misalta wannan haihuwa a matsayin matabbaciyar alama ta nasara ga dukkanin 'yan takara na jam'iyyar PDP a kowane mataki, inda ya sha alwashin budewa jaririyar asusun ajiya da Naira Miliyan wanda za ta ci moriya yayin da ta kai mataki na hankali.

Ya shawarci al'umma da su tabbatar da kariya ga kuri'un su yayin zabe tare da neman su akan riko da akidar nan ta a tsaya a raka, kuma a jira a tabbatar. Ya kuma gargade su kan mallakar makamin su na 'yanci da ya kasance katin zabe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel