Yanzu Yanzu: Wata kungiya na zanga-zanga a majalisar dokokin Lagas kan shirin tsige Gwamna Ambode

Yanzu Yanzu: Wata kungiya na zanga-zanga a majalisar dokokin Lagas kan shirin tsige Gwamna Ambode

Wata kungiyar masu zanga-zanga a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu ta kai mamaya majalisar dokokin jihar Lagas domin yin zanga-zanga akan shirin tsige gwamnan jihar, Akinwunmi Ambode.

Masu zanga-zangar a cewar wani rahoto a jaridar The Nation, sun kasance dauke da walayen sanarwa da rubuce daban-daban na fafutukarsu.

Legit.ng ta tattaro cewa majalisar dokokin jihar ta zargi Ambode da saba dokoki wajen sanya hannu a dokar kasafin kudin 2019.

Yanzu Yanzu: Wata kungiya na zanga-zanga a majalisar dokokin Lagas kan shirin tsige Gwamna Ambode

Yanzu Yanzu: Wata kungiya na zanga-zanga a majalisar dokokin Lagas kan shirin tsige Gwamna Ambode
Source: UGC

A baya mun ji cewa Majalisar dokokin jihar Legas na cikin zama da yammacin ranar Litinin, 28 ga watan Junairu, 2019 domin tsige gwamnan jihar, Akinwumi Ambode, bisa ga laifi da suka zarginshi da shi.

Mun samu wannan rahoto ne daga gidan talabijin ta TVC da ke zaune a Legas in tace: "Yan majalisa suna shirin tsige gwamna Akinwumi Ambode, suna zargin da laifuka."

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin sama ta lalata sansanin dabaru na Boko Haram a dajin Sambisa

Yanzu Yanzu: Wata kungiya na zanga-zanga a majalisar dokokin Lagas kan shirin tsige Gwamna Ambode

Yanzu Yanzu: Wata kungiya na zanga-zanga a majalisar dokokin Lagas kan shirin tsige Gwamna Ambode
Source: UGC

Yan majalisan suna zargin gwamnan da kashe wasu kudade ba tare da sa hannun majalisar dokokin jihar ba. Gwamna Ambode ya shiga tarkon jama'an jiharsa ne yayinda aka fara zarginsa da daukar nauyin dan takarar gwamnan PDP, Jimi Agbaje, a zaben da zai gudana a watan Maris.

A baya, an yi masa barazanar tsigeshi jim kadan bayan ya sha kasa a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC inda kwamishana da ke karkashinsa, Babajide Sanwoolu, ya kashe zaben.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel