Majalisin Alkalan kasar nan (NJC) kawai ya sallami Onnoghen - Falana

Majalisin Alkalan kasar nan (NJC) kawai ya sallami Onnoghen - Falana

- Falana ya hori NJC da ta umarci Onnoghen ya koma gefe har zuwa lokacin da za a kammala shari'ar shi

- Yace ba zai biyewa NBA ba don ba zai yiwa laifi kara ba

- Duk da ya kushe dakatar da alkalin alkalan amma NJC yakamata tayi abinda zai hana ta tozarta

Majalisin Alkalan kasar nan (NJC) kawai ya sallami Onnoghen - Falana

Majalisin Alkalan kasar nan (NJC) kawai ya sallami Onnoghen - Falana
Source: Depositphotos

Lauya mai kare hakkin Dan Adam Femi Falana (SAN) ya hori NJC da tasa dakataccen alkalin alkalai, Walter Onnoghen da ya ja gefe har zuwa lokacin da za a gama shari'ar shi.

Falana yace ya kai ga matsayar shi ne bayan da ya san cewa duk masu shari'a da aka kama da laifi kuma aka kaisu kotu sukan dakata daga aiyukan shari'a har sai an kammala shari'ar su.

Ya zargi kungiyar lauyoyi ta kasa da yin fuska biyu ta hanyar kalubalantar dakatar da mai shari'a Onnoghen.

Falana yace ba daidai bane ace NBA wacce tayi kira akan dakatar da masu shari'a da cibiyoyin tsaro suka kama a 2016 amma su ce abar alkalin alkalai a kujerar shi.

Falana, wanda yake fuskanta a babban kotun tarayya don halartar wata shari'a yayi kunnen uwar shegu da umarnin NBA na cewa lauyoyi kada suje Kotu, yace lauyoyi da yawa sunki bin umarnin, kuma sunje kotun.

GA WANNAN: Tsugunne bata qare ba, inji NLC, duk da cewa manyan Janar din Najeriya sun tantance

Yace: "Inada shari'a a gaban babbar kotun tarayya. Na baro Legas jiya don zuwa kotu. Wadanda suka dauke ni na tare dani kuma uzirin su ya wuce na NBA. Ina zaton zamuyi zaman kotun amma alkalin bai zo ba saboda yaje wani taro saboda shirin komawa kotu akan shari'ar Onnoghen. Amma gaskiya ni bazan bi umarnin NBA ba."

"Na kushe dakatar da alkalin alkalan Najeriya wanda umarnin CCT ne. Amma kuma na bukaci da a dage dakatarwar. Na kuma roki alkalin alkalan da yayi abinda ya dace na sauka daga kujerar shi. Kuma ina tunanin akwai damar yin abinda ya dace."

A dalilin shi na zuwa kotu a ranar da NBA tace duk lauyoyi suyi wa kotu yaji, Falana yace a matsayar shi dai bazai iya tausar kanshi ba "yayi wa laifi kara ba"

"Yakamata ace NJC tayi taro a ranar 15 ga watan Janairu, ranar talata kenan ta satin da ya gabata kuma da kungiyar ta kare kanta da aikin ta daga abin kunyar. Naji dadi da wasu da wasu wadanda suka damu suka kara sa taron yau." Inji Falana.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel