Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da shugaban jam'iyyar APC na a jihar Adamawa

Yanzu-yanzu: An yi garkuwa da shugaban jam'iyyar APC na a jihar Adamawa

An yi garkuwa da shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na karamar hukumar Demsa na jihar Adamawa, Hamisu Mijinyawa.

Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da Mijinyawa ne misalin karfe 1:00 na daren ranan Talata gabanin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa da gwamnan a karamar hukumar Demsa.

A yanzu haka, ana sauraron zuwan gwamnan jihar Adamawa, Jibrilla Bindow, a karamar hukumar domin yakin neman zaben.

Wani jigon jam'iyyar APC a jihar, Mark Dauda, ya tabbatar da garkuwa da shugaban jam'iyyar kuma ya ce sun bayyana kudin da suke bukata matsayin fansa.

Yace: "An sace shugabanmu a gidansa dake Demsa misalin karfe daya na daren jiya, amma muna magana dasu kan sakinsa."

"Sun bukaci fansan miliyan ashirin, abinda zan iya fadi yanzu kenan."

KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar Jastis Walter Onnoghen

A jiya Litinin kuwa, an yi garkuwa da shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC na jihar Abia, Chief Donatus Nwamkpa, yayinda mutan jihar ke sauraron zuwan shugaba Muhammadu Buhari jihar domin yakin neman zabensa karo na biyu.

Kakakin jam'iyyar APC na jihar, Kwamred Benedict Godson, ya tabbatar da haka ga jaridar Daily Trust da safiyar nan.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa kakakin hukumar yan sandan jihar Abiya, Geoffrey Ogbonna, ya ce an tura akalla jami'an yan sanda 1000 domin tabbatar da tsaro yayinda shugaba Buhari zai kawo ziyara jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel