Rundunar sojin sama ta lalata sansanin dabaru na Boko Haram a dajin Sambisa

Rundunar sojin sama ta lalata sansanin dabaru na Boko Haram a dajin Sambisa

Rundunar sojin sama na Operation Lafiya Dole sun lalata sansanin dabarun yan ta’addan Boko Hara a dajin Sambisa, jihar Borno.

Legit.ng ta tattaro cewa an gudanar da aikin ne a ranar Litinin, 28 ga watan Janairu bayan wani bincike na fannin kwararru ya bayyana kasancewar mutane da alamun ababen hawa a sansanin dabarun, wanda aka yasar a wajen.

Don haka, rundunar sojin sama ta tura jiragen yaki biyu don su kai hari wajen, wata sanarwa daga kakakin rundunar sojin sama, Air Commodore Ibikunle Daramola zuwa ga yan jarida ya bayyana.

Rundunar sojin sama ta lalata sansanin dabaru na Boko Haram a dajin Sambisa

Rundunar sojin sama ta lalata sansanin dabaru na Boko Haram a dajin Sambisa
Source: Twitter

Don haka sojojin suka far ma yankin sannan suka kaddamar da hari akan yan ta’addan. An gano wasu daga cikin yan ta’addan da suka tsira daga harin suna ta gudu don tsira, amma an shafe su a harin da sojin suka sake kaddamarwa a kansu.

KU KARANTA KUMA: Mutane da dama sun mutu, motoci sun kone yayinda tankar fetur ta tashi

A baya mun ji cewa Sakamakon wani hadin gwiwar da akayi tsakanin sojin Najeriya dake bataliya ta 114 da kuma sojojin sakai da kuma yan kato-da-gora a ranar lahadi 19 ga wata sun kai samame a garin Bitta-Damboa.

Wata sanarwar da rundunar sojojin ta fitar ta ce sojojin sun kaddamar da wani hari daga garin Bitta har Gambori dake jihar Borno.

Sanarwar ta cigaba da cewa yayin samamen da aka kai anyi arangama da yan ta'addan Boko Haram din a kauyen Bulajani inda kuma aka samu nasarar kora tare da kashi su baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel