Shehu Sani yace da El-Rufai aka ci romon PDP, yanzu ya dawo yana sukar barnar Jam'iyyar

Shehu Sani yace da El-Rufai aka ci romon PDP, yanzu ya dawo yana sukar barnar Jam'iyyar

Mun samu labari cewa Sanatan Kaduna ta tsakiya watau Kwamared Shehu Sani ya bayyana cewa nan gaba kadan sai gwamna Malam Nasir El-Rufai ya juyawa shugaban kasa Muhammadu Buhari baya.

Shehu Sani yace da El-Rufai aka ci romon PDP, yanzu ya dawo yana sukar barnar Jam'iyyar

El-Rufai zai fara sukar Buhari nan gaba kadan inji Sanatan Kaduna
Source: Depositphotos

Sanata Shehu Sani ya bayyana wannan ne a lokacin da yayi hira da Osasu Igbinedion a cikin shirin nan na Osasu Show. Sanatan yace da zarar Buhari ya bar kan kujerar mulki, Nasir El-Rufai zai juya masa baya kamar yadda ya saba.

‘Dan Majalisar wanda yake ta faman sa-in-sa da gwamnan na sa tun 2015, ya bayyana cewa gwamnan na Kaduna ya saba juyawa duk shugaban da ya bar kan karagar mulki baya. Yanzu dai El-Rufai yana tare da Shugaba Buhari.

KU KARANTA: Onnoghen: Bola Tinubu yayi kaca-kaca da ‘Dan takarar PDP Atiku

Fitaccen Sanatan ya fadawa ‘yan jarida cewa su ajiye hirar da aka yi da shi domin ko ba jima, ko ba dade kuwa, sai an ji gwamna Nasir El-Rufai yana yin dai-daya da shugaban kasa Buhari wata rana, Sanatan yace lokaci kurum ake jira.

Sanatan na PRP yake cewa da wuya ya iya aiki da gwamnan a nan gaba inda yake cewa da irin su Nasir El-Rufai aka ci shekaru kusan 14 cikin shekarun da PDP tayi tana mulki, sai kuma daga baya ya koma APC yana sukar jam’iyyar adawar.

‘Dan Majalisar wanda ya bar APC kwanaki yace haka El-Rufai ya rika sukar Obasanjo bayan ya bar gwamnati, ya kuma ce haka aka yi tsakanin sa da Jonathan da Marigayi ‘Yaradua bayan ya samu sabani da su a lokacin su na kan mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel