Yanzu Yanzu: Mutane 2 sun mutu, motoci sun kone yayinda tankar fetur ya tashi

Yanzu Yanzu: Mutane 2 sun mutu, motoci sun kone yayinda tankar fetur ya tashi

- Wani motar tanka dauke da man fetur lita 33,000 ya fadi a Barracks bus stop, hanyar babban titin Mile 2/Badagry, yankin Ojo da ke jihar Lagas

- An tabbatar da mutuwar mutane biyu, mace da namiji sannan ababen hawa da dama ma sun kone

- Fetur din da ke cikin tankar ya barbazu a kasa sannan ya kama da wuta bal-bal

Abun bakin ciki ya faru a safiyar ranar Laraba, 30 ga watan Janairu,lokacin da wani motar tanka dauke da man fetur lita 33,000 ya fadi a Barracks bus stop, hanyar babban titin Mile 2/Badagry, yankin Ojo da ke jihar Lagas.

Fetur din da ke cikin tankar ya barbazu a kasa sannan ya kama da wuta bal-bal, jaridar Guardian ta ruwaito.

Mutane da dama sun mutu, motoci sun kone yayinda tankar fetur ta tashi

Mutane da dama sun mutu, motoci sun kone yayinda tankar fetur ta tashi
Source: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa an tabbatar da mutuwar mutane biyu, mace da namiji a wannan mumunan lamarin, wanda ya kuma yi sanadiyan konewar ababe hawa da dama.

A cewar rahoton, jami’an yan sanda, jami’an hukumar kashe gobara, da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa na Lagas (LASEMA) na a wajen don aikin ceto.

Idanun shaida sun bayyana cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 5am na asuba.

KU KARANTA KUMA: Ka fadawa duniya kadarorin da ka mallaka – Afenifere ga Buhari

A baya mun ji cewa an samu asarar dukiya mai yawa sakamakon tashin gobara a babban kasuwar birnin Jalingo fadar jihar Taraba, da yammacin ranar Talatar da ya gabatar, sai dai babu asarar rai amma mutane da dama sun samu raunuka, wanda a karshe akayi nasarar kashewa.

Gobarar da ake kyautata zaton cewa ya soma ne a ɗaya daga cikin irin injuna da ƴan kasuwan ke amfani dasu wurin samun hasken wutar lantarki a kasuwar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel