Kamfanin MTN na neman Miliyan 5 daga wajen Gwamnatin Kogi

Kamfanin MTN na neman Miliyan 5 daga wajen Gwamnatin Kogi

Mun samu labari daga wata jaridar kasar nan cewa Kamfanin MTN ya kai karar gwamnatin jihar Kogi gaban kotu inda su ke neman a biya su wasu miliyoyin kudi. Wani jami’in kamfanin ya fadi haka.

Kamfanin MTN na neman Miliyan 5 daga wajen Gwamnatin Kogi

Kamfanin MTN sun kai karar Gwamnatin Jihar Kogi gaban Alkali
Source: Twitter

Kamfanin sadarwa na MTN ya maka gwamnatin Kogi a kotu ne a dalilin rufe masu wasu kayan aiki da hukumar karbar haraji ta jihar Kogi tayi kwanaki. Wannan abu da gwamnatin jihar tayi ya jawowa kamfanin mugun asara.

Tobechukwu Okigbo, wanda babban jami’in kamfanin ne ya bayyana wannan jiya a lokacin da ya zanta da manema labarai a Garin Legas. Okigbo yace kwamishinan shari’a na jihar da kamfanin NCC su na cikin wadanda ake kara.

KU KARANTA: An yi sulhu bayan MTN zai biya Bankin CBN kudi har Dala Miliyan 50

MTN sun shigar da karar ne a babban kotun tarayya da ke babban birnin jihar Kogi watau Lokoja. Kamfanin sun koka da cewa jami’an haraji sun garkame masu kayan aiki a farkon watan nan duk da su na da lasisin kasuwanci a jihar.

Babban jami’in kamfanin sadarwar yace babu wani bashi da hukumar ta KGRIS mai karbar haraji ta ke bin su, don haka su ka nemi kotu ta bayyana haramcin rufe masu kayan aiki da aka yi makonni kusan 4 da su wuce babu gaira babu dalili.

Okigbo yana neman Alkali mai shari’a ya nemi gwamnatin Kogi ta ba su miliyan 5 domin su rage asara a dalilin hana su neman kudi da aka yi ba tare da wata hujja a dokar jihar Kogi ko kuma ta Najeriya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel