Yadda aka bindige wani matashi har lahira saboda rabon kudin kamfen

Yadda aka bindige wani matashi har lahira saboda rabon kudin kamfen

Wani matashi da ke ajin karshe a Jami'ar Jihar Bayelsa mai suna James Eze ya rasa ransa a ranar Litinin yayin da dan wani kungiyar ya bindige shi har lahira saboda ya ki bashi kudin yakin neman zabe da wata jam'iyya ta bayar a raba.

Eze, ya yanke jiki ya fadi cikin 'yan mintuna bayan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar People’s Democratic Party, PDP sun bar unguwt Famgbe da ke karamar hukumar Yenagoa na jihar Bayelsa kamar yadda Punch ta ruwaito.

Wani wanda abin ya faru a gabansa amma bai amince a fadi sunansa ba ya ce matashin suna musayar maganganu ne da wasu kungiyoyin a kan yadda za a raba kudin da aka bayar kwatsam sai wani ya dirka masa harsashi.

Yadda aka bindige wani matashi har lahira saboda rabon kudin kamfen

Yadda aka bindige wani matashi har lahira saboda rabon kudin kamfen
Source: Twitter

DUBA WANNAN: NJC ta kammala taron gaggawa, tayi hukunci a kan Muhammad da Onnoghen

An ruwaito cewar 'yan jam'iyyar na PDP sunyi gaba bayan anyi harbin bindiga kana 'yan kungiyoyin suka fara musayar wuta a tsakaninsu wadda hakan ya janyi rudani a unguwar.

Majiyar ya ce, "Muna zaune a gefe muna kallon kamfen din sai muka ga an mika wa Eze kudi a yayin da masu kamfen din ke shirin tafiya, kwatsam sai 'yan wata kungiyar daban suka bayyana inda suka nemi ya mika musu kudin.

"Matashin ya ki mika kudin kuma hakan yasa wani ya harbe shi nan take a hannun da ya ke rike jakar kudin kuma ya sake harbinsa a kirjinsa.

"Hakan yasa 'yan kungiyarsa suma suka zaburo cikin gaggawa domin yin ramako wadda hakan ya janyo suka rika musayar wuta tsakaninsu. Babu wanda ya sake mutuwa amma wasu sun jikkata sai dai ban san adadinsu ba a yanzu."

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Asinim Butswat ya ce bai samu rahoton afkuwar lamarin ba daga hedkwatan 'yan sanda na Yenagoa amma ya yi alkawarin zai tuntubi 'yan jarida da zarar ya samu bayani.

Bai sake yin wani bayani ba a yayin rubuta wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel